Ganawar Gwamna Wike da Wasu Gwamnonin Tsaginsa Ya Kara Hargitsa Jam'iyyar PDP

Ganawar Gwamna Wike da Wasu Gwamnonin Tsaginsa Ya Kara Hargitsa Jam'iyyar PDP

  • Cikin shugabannin PDP ya duri ruwa sakamakon shirun da gwamnonin tsagin Nyesome Wike suka yi
  • Gwamnonin jam'iyyar biyar sun sa labule a ranar Lahadi a jihar Enugu, kuma ana ta zuba idon jin matsayin su amma kuma sun yi biris
  • Gwamnonin sune Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Wike na Ribas

Abuja - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shirun da gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) biyar masu biyayya ga tsagin Nyesome Wike na jihar Ribas suka yi ya sa cikin shugabannin jam’iyyar ya duri ruwa.

A ranar Lahadi ne gwamnonin da suka hada da Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Wike suka gana a Enugu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: APC Ba Ta Da Halastacen Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Ku Zabi Atiku, PDP Ga Yan Najeriya

An rahoto cewa sun saka labulen ne domin daukar matsaya kan rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawar kasar.

Gwamnonin PDP
Ganawar Gwamna Wike da Wasu Gwamnonin Tsaginsa Ya Kara Hargitsa Jam'iyyar PDP Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Gwamnonin da wasu na hannun damarsu na ta caccar baki da shugabannin jam’iyyar tun bayan da aka zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike da yan kanzaginsa sun bukaci lallai sai Iyorchia Ayu ya yi murabus daga matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, sannan a maye gurbinsa da wani dan kudu don yin adalci wajen rabon mukamai.

Sun ce yankin arewacin kasar ya fi kwasan kaso mai tsoka a wajen rabon mukaman shugabancin jam’iyyar.

Wani jigon jam’iyyar ya fada ma jaridar Daily Trust cewa a yanzu haka suna nan suna jiran sakamakon kokarin da kwamitin sulhu na kwamitin amintattu na jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Adolphus Wabara ke yi.

Kara karanta wannan

2023: "Da Sauran Matsala" Jigon PDP Ya Fallasa Gaskiyar Abinda Ya Faru a Taron Wike da BoT

Kwamitin amintattun ya gana da gwamnoni da dama, Okowa da Atiku, kuma ana sa ran zai gana da Wike a yau don yiwa tufkar hanci.

A cewar majiyar:

“Komai a yanzu ya dogara ne ga kokarin sulhi na kwamitin amintattu, bayan ganawa tsakanin Atiku da Wike a ranar Alhamis.
“Mutane da dama sun zata gwamnonin zasu bayyana matsayinsu bayan ganawar da suka yi a ranar Lahadi a Enugu, amma a halin yanzu babu wanda ke da tabbass.”

Wata majiya a hedkwatar jam’iyyar ta bayyana cewa Atiku da BoT ne kadai za su iya sulhunta wannan lamari yadda lamuran suke a yanzu.

Legit.ng ta tuntubi wani masanin yadda harkokin siyasar kasar ke gudana a yanzu haka inda yace kamata yayi abi rikicin da ya dabaibaye PDP a sannu.

Ya ce:

"Rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP tsakanin tsagin ɗan takarar shugaban ƙasarta Atiku Abubakar da tsagin Gwamna Wike na jihar Ribas abu ne da ya kamata a bi shi sannu a hankali don kada a ƙara uzzura rikicin.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Gwamnoni 18 a Najeriya Sun Koma Bayan Takarar Peter Obi a Zaben 2023

"Sanin kowa ne cewa gwamnoni na taka rawar gani wajen zaɓen shugaban ƙasa domin kuwa su ke kawo ma ɗan takarar shugaban ƙasa jiharsu, saboda haka yawan gwamnoninka yawan ƙuri'un da kake sa rai waɗanda zasu baka nasara a zaɓe a matsayinka na ɗan takarar shugaban kasa.
"Saboda haka ya zama wajibi akan PDP da Atiku su bi gwamnonin nan 5 da hikima wajen warware wannan taƙaddamar. Gwamnonin kuwa su ne; Seyi Makinde (Oyo), Samuel Ortom (Benue), Okezie Ikpeazu (Abia) Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) da jagoransu Nyesom. Wike.
"Musamman duba da cewa Ribas, Abia da Enugu jihohi da zasu yi ma PDP da Atiku sauƙin ci idan har ya sun samu goyon bayansu. Haɗi da cewa Ribas na cikin jerin jihohi 5 masu yawan ƙuri'u a Najeriya.
"A yanzu dai gwamnonin sun gana a jihar Enugu, amma basu sanar da matsayin da suka ɗauka ba. Koma dai menene matsayinsu, fatan Atiku shi ne kowa ya mayar da wuƙarsa cikin kube su mara baya ya kai labari a karawar da zai yi da Tinubu, wanda a yanzu ya ɗaure gwamnonin jam'iyyarsa APC a karkashin tsintsiyarsu."

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC 6 Kan Rikicin Kwamitin Kamfe

Gwamnonin Jam’iyyar PDP 5 Sun Yi Ganawar Sirri A Enugu, Hotuna

A baya mun kawo cewa wasu daga cikin manyan gwamnonin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun yi wata ganawar sirri a jihar Enugu a ranar Lahadi, 2 ga watan Oktoba, jaridar The Nation ta rahoto.

Jaridar Sun ta rahoto cewa tattaunawarsu ta karkata ne kan yadda zasu kawowa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Mista Peter Obi, kuri'u a zaben 2023.

Gwamnonin da suka halarci wannan zama sun hada da na jihar River, Nyesome Wike, Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Online view pixel