Sauya Sheka: Bola Tinubu da Uba Sani Sun Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Mambobin PDP a Kaduna

Sauya Sheka: Bola Tinubu da Uba Sani Sun Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Mambobin PDP a Kaduna

  • Gabannin zaben 2023, jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta rasa mambobinta masu yawan gaske a jihar Kaduna
  • Dumbin mutanen da suka sauya sheka daga jam'iyyar adawar sun koma bayan Sanata Uba Sani da Bola Ahmed Tinubu na APC
  • Masu sauya shekar sun sha alwashin yin aiki tukuru domin ganin Uba Sani ya dare kujerar gwamnan jihar a zabe mai zuwa

Kaduna - Dubban masu sauya sheka daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) sun koma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna.

Masu sauya shekar, sun sha alwashin tabbatar da nasarar Sanata Uba Sani da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a babban zaben 2023 mai zuwa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Uba Sani da Shettima
Sauya Sheka: Bola Tinubu da Uba Sani Sun Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Mambobin PDP a Kaduna
Asali: Original

Sanata Uba Sani mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa kuma dan takarar gwamna na APC, ya bayyana cewa kokarinsa na shiga Kashim Ibrahim House ya samu gagarumin goyon baya a karshen makon.

Ya ce kungiyar yan kasuwa na arewa tare da hadin gwiwar kungiyar yan kasuwa a jihar Kaduna daga kananan hukumomi 23 na jihar sun ayyana goyon bayansu ga takararsa da na Bola Tinubu da daukacin APC a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan takarar gwamnan ya ce:

“Yayin da nake jawabina a taron, na yi godiya ga kungiyar kan haduwa da suka yi don ayyana goyon bayansu ga takarata da APC a jihar Kaduna.”

Uba Sani ya kuma baiwa yan kasuwa tabbacin ci gaba da kokarin gwamnati mai ci na bunkasa tattalin arzikin jihar Kaduna.

Ya sha alwashin ci gaba da tallafi ga karin yan kasuwa wadanda ke bukatar jari a kasuwanci.

Atiku Ya Sake Shiga Tasku, Wasu 'Ya'Yan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC Ana Tsaka da Rikici

A wani labarin, mun ji cewa wasu mambobin jam’iyyar siyasa a jihar Oyo sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin babban zaben 2023.

Masu sauya shekar sun samu tarba a ranar Asabar yayin wani taron jam’iyyar da ya gudana a makarantar sakandare na Elekuro, Ogbere a yankin Ona-Ara da ke jihar.

Wadanda suka jagoranci taron na maraba da zuwa sune, Sanata Teslim Folarin, dan takarar gwamna na APC a jihar da Dr Yunus Akintunde, dan takarar sanata mai wakiltan Oyo ta tsakiya, PM News ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel