Yan Bindiga Sun Budewa Motocin Tawagar Kamfen Sanata Uba Sani Wuta A Kaduna, An Sace Jiga-Jigan APC

Yan Bindiga Sun Budewa Motocin Tawagar Kamfen Sanata Uba Sani Wuta A Kaduna, An Sace Jiga-Jigan APC

  • Yan bindiga sun budewa jiga-jigan jam'iyyar APC a Kaduna wuta kuma sun sace mutum biyu
  • Tawagar sun tafi kudancin Kaduna ganawa da Fastoci ne gabanin fara yakin neman zabe
  • An yi garkuwa da dan takaran majalisa da kuma mataimakin shugaban APC na karamar hukuma

Kaduna - Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da wasu jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a babban titin Kaduna-Kachia a jihar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito cewa harin ya auku ne a Tashar Icce, kusa da garin Kujama dake karamar hukumar Kajuru.

Tawagar jiga-jigan na hanyarsu ta komawa gida ne bayan ganawa da jagororin Kiristoci a kudancin Kaduna ranar Alhamis.

A cewar Daily Trust, daya daga cikin yan siyasan da ya tsallake rijiya da baya yace kimanin motoci biyar yan bindigan suka budewa wuta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gobe Juma'a Zan Tona Asirin Wasu Shugabannin Jam'iyyar PDP, Nyesom Wike

Ya ce an yi awon gaba da mutum biyu yayinda wasu mutum uku suka jikkata.

An tattaro cewa dan takaran gwamnan jihar Sanata Uba Sani, bai cikin motar saboda ya tafi Abuja daga Kafanchan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kaduna
Yan Bindiga Sun Budewa Motocin Tawagar Kamfen Sanata Uba Sani Wuta A Kaduna, An Sace Jiga-Jigan APC
Asali: UGC

Diraktan Kamfensa, Sani Maina, Ahmed Mayaki, da wasu jigogin jam'iyyar sun tsira.

Daga cikin wadanda aka sace sune dan takaran kujeran majalisar jiha na Kajuru, Mr Madaki, da kuma mataimakin shugaban jam'iyyar APC na Kajuru, Ruben Waziri.

Ben Maigari, wani dan'uwan Ruben Waziri, yace har yanzu yan bindigan basu tuntubi iyalansa ba.

A cewarsa:

"An kai musu hari; yan bindigan sun tare hanyar kuma suka bude musu wuta. An sace dan'uwana, Ruben, tare da Madaki saboda suna cikin mota daya."

Legit Hausa ta yi yunkurin tuntuban Kakakin hukumar yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalinge.

Ya bayyana cewa zai nemi karin bayani kan lamarin kuma zai tuntubemu.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnoni, tsaffin ministoci, jiga-jigai masu goyon bayan Wike sun yi hannun riga da kwamitin kamfen PDP

Yace:

"Bari zan kira ka"

Har yanzu dai yayin wallafa labarin basu ji daga garesa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel