Rikicin Ya Barke A NNPP, An Rushe Shugabancin Jam'iyya Na Wata Jiha

Rikicin Ya Barke A NNPP, An Rushe Shugabancin Jam'iyya Na Wata Jiha

  • Hedkwatar jam'iyyar NNPP na kasa ta rushe shugabannin jam'iyyar na reshen Jihar Osun saboda rikici da ya barke a jihar
  • Mambobin jam'iyyar sun kada kuri'ar rashin gamsuwa ga shugaban jam'iyyar na jiha, Dipo Olayoku bayan zarginsa da laifuka masu alaka da karkatar da kudade
  • Kwamitin NWC ta kuma nada wata kwamitin rikon kwarya a jihar karkashin bdulasalam Abdulateef wacce za ta jagoranci jam'iyyar na wata uku

Osun - Kwamitin ayyuka na kasa, NWC, ta jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta soke shugabanninta na jihar Osun saboda rikicin shugabanci, rahoton Premium Times.

Rushe shugabannin na dauke ne cikin wata wasika mai kwanar wata na 11 ga watan Satumba da sa hannun sakataren jam'iyyar na kasa, Dipo Olayoku.

Tambarin NNPP
Rikicin Ya Barke A NNPP, An Rushe Shugabancin Jam'iyya Na Jihar Osun. Hoto: @PremiumTimesNG.
Asali: Twitter

Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta samu kwafin wasikar a ranar Talata a Osogbo.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An rushe shugabannin jihar ne bayan kuri'ar rashin goyon baya da aka kada wa shugaban jam'iyyar, Tosin Odeyemi, da murabus da mambobinsa da dama suka yi.

NWC din ta kafa kwamitin mutum shida na rikon kwarya a madadin shugabannin da aka rushe.

Kwamitin za ta rika kula da jam'iyyar na tsawon wata uku karkashin jagorancin Abdulasalam Abdulateef.

Wani sashi na wasikar ya ce:

"Bayan nazarin abubuwan dake faruwa a NNPP na Osun da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki, NWC ta amince da rushe shugabannin jihar.
"Hedkwatar ta lura cewa kalilan daga cikin shugabannin jam'iyyar a jihar Osun suka rage saboda murabus da suka ta yi.
"Sauran mambobin sun cire tsammani kan jagorancin ciyaman, Dr Tosin Odeyemi, na samar da shugabanci da ake bukatar gabanin babban zaben 2023."

Ta cigaba da cewa:

"Ana iya ganin hakan saboda kuri'ar rashin gamsuwa da shugabannin suka yi wa tsohon ciyaman.

Kara karanta wannan

PDP: Gaskiyar Dalilin Da Yasa Gwamnoni Suka Ki Zuwa Taron Jam’iyya A Abuja

"NWC na amfani da wannan damar don kira ga shugaban kwamitin rikon kwaryar da sauran mambobi su nuna halayen jagoranci na gari kuma suyi amfani da wannan damar don haka kan yan jam'iyya.
"NWC tana kira ga yan jam'iyyar a Osun su kwantar da hankulansu su saurari umurni daga hedkwata na kasa."

Martanin shugaban kwamitin rikon NNPP a Osun

Da aka tuntube shi, shugaban kwamitin rikon ya ce zai yi amfani da wannan damar don hada kan mambobin jam'iyyar gabanin babban zaben 2023.

Mr Abdulateef ya ce mambobin kwamitin rikon za su yi amfani da wa'adinsu don bincike kan dalilin da yasa NNPP na Osun ke jan kafa kuma su yi aiki don nasarar dan takarar shugaban kasarsu Alhaji Rabiu Kwankwaso.

Ya ce:

"Dole mu hada kai kuma mu zama masu alkibla.
"Dole dukkanmu mu hada hannu mu san cewa akwai wani abu a gaban mu kuma mu yi shi da adalci don nasarar jam'iyyar mu."

Kara karanta wannan

Da Dumi: Rikicin PDP Ya Dau Sabon Salo, Wasu Yan Majalisar NWC Sun Bijirewa Ayu, Walid Jibrin Shima Zai Yi Murabus

Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa

A wani rahoton, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, da jami'an tsaro suka yi a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel