Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa

Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa

  • Sanata Rabi'u Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya yi tir da rufe sabon sakateriyar jam'iyyarsu da aka yi a Borno
  • Tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyar ta NNPP su kwantar da hankulansu a yayin da ake kokarin warware matsalar
  • Rufe hedkwatar na zuwa ne a lokacin da ake shirin Kwankwason zai ziyarci Jihar Borno a cikin yan kwana-kwanan nan don kaddamar da ofishin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Twitter - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shuganan kasa na jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, da jami'an tsaro suka yi a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

NNPP Office Borno
Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa. Hoto: @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 25 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na Jihar Kano ya yi Allah-wadai da matakin.

Kara karanta wannan

2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Zabi Dan Siyasan Arewa Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma, duk da hakan ya yi kira ga magoya bayan jam'iyyarsu ta NNPP su kwantar da hankulansu tare da kasancewa masu bin doka da oda a yayin da suke kokarin warware matsalar.

Kalamansa:

"Rufe hedkwatar jam'iyyar mu na Maiduguri da gwamnatin Jihar ta yi abin Allah-wadai ne baki dayansa.
"Duk da wannan abin mara dadi, ina kira ga magoya bayan mu su kwantar da hankulansu, su zama masu bin doka a yayin da muke kokarin warware matsalar."

Martanin shugaban APC na Borno

Sai dai shugaban jam'iyyar APC na Jihar Borno, Ali Bukar Dalori ya musanta cewa APC na da hannu a lamarin kamar yadda Attom ya yi ikirari.

Ya ce:

"Ina son tabbatar maka, APC ta Jihar Borno bata da hannu cikin rufe sakateriyar NNPP kamar yadda Honarabul Attom ya yi ikirari.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Sanda Sun Rufe Sabuwar Ofishin NNPP A Borno, An Kuma Kama Shugaban Jam'iyyar

"Yanzu na ke jin labarin daga wurinka, kuma idan Honarabul Attom yana hannun yan sanda, suyi kokari su sulhunta kansu, amma kada ya saka jam'iyyar mu ciki."

Kwankwaso: Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba Kuma Ban Tura Mataimaki Na Ya Wakilci Ni Ba

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa bai halarci bikin bude taron kungiyar lauyoyi na Najeriya, NBA, na 2022 da aka yi a Legas ba.

Rahotanni sun nuna cewa dan takarar APC, Bola Tinubu da Kwankwaso ba su halarci taron ba duk da cewa yan takarar shugaban kasa na manyan jami'iyyu a kasar sun hallarci taron da aka yi a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel