Rikicin PDP Ya Dau Sabon Salo, Wasu Yan Majalisar NWC Sun Bijirewa Ayu, Walid Jibrin Shima Zai Yi Murabus

Rikicin PDP Ya Dau Sabon Salo, Wasu Yan Majalisar NWC Sun Bijirewa Ayu, Walid Jibrin Shima Zai Yi Murabus

  • Majiyoyi sun bayyana cewa wasu mambobin kwamitin sun juyawa shugaban jam'iyyar baya
  • Suna tuhumarsa da kin bayyana kudaden da ya samu daga wajen wasu yan takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar
  • Ana zaune kuma shugaban kwamitin dattawan jam'iyyar ya sanar da niyyar murabus daga kujerarsa

Abuja - Rikicin jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ya dau sabon salo yayinda mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar suka bijirewa shugaba Iyorchia Ayu.

Mambobin sun ce daga yanzu ba zasu sake halartan duk zaman da shugaban jam'iyya, Iyorchia Ayu, ya shirya ba.

Hakazalika Shugaban majalisar amintattu da dattawa jam'iyyar PDP, Walid Jibrin, ya shirya murabus daga kujerarsa kai tsaye, rahoton TheCable.

Jibrin ya rike wannan kujera tsawon shekaru shida yanzu tun bayan cire Halliru Bello a shekarar 2016.

Kara karanta wannan

Hotuna: Kwankwaso Ya Ziyarci Jihar Benue, Ya Aiwatar Da Muhimmin Aiki

Walid
Rikicin PDP Ya Dau Sabon Salo, Yan Majalisar NWC Sun Bijirewa Ayu, Walid Jibrin Shima Zai Yi Murabus Hoto: PDP
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa tuni Walid Jibrin ya sanar da masu ruwa da tsakin jam'iyyar kan niyyar murabus dinsa.

Daya daga cikin majiyoyin yace:

"Yace zai yi hakan ne don zaman lafiya a jam'iyyar tun da wasu na korafin ana bangaranci."

Shugaban jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu, dan takarar kujeran shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar, da Shugaban kwamitin amintattu Walid Jibrin duka yan Arewacin Najeriya ne.

Abinda ya sa ake kira ga Ayu yayi murabus

A 2021, Ayu yayi alkawarin cewa zai yi murabus matsayin shugaban uwar jam'iyyar PDP idan dan Arewa ya zama dan takaran shugaban kasa.

Amma bayan nasarar Atiku, Iyorchia Ayu ya ce ba zai yi murabus ba kuma masu cewa yayi kananan yara ne.

Yanzu wasu mambobin NWC sun bijire masa.

Suna tuhumarsa da kin bayyana kudaden da ya samu daga wajen wasu yan takara a zaben fidda gwanin jam'iyyar da aka yi a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babban Jam'iyya A Najeriya Ta Dakatar Da Dan Takarar Shugaban Kasarta

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa mambobin kwamitin gudanarwan sun ce basu tare da Ayu.

Sunce basu ji dadin irin kalaman da Ayu yayi na kiran wasu mambobin jam'iyyar yara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel