Ana Rade-Radin Tinubu Yana Rigima da Shugaban APC, Jam’iyya Tayi Karin Haske

Ana Rade-Radin Tinubu Yana Rigima da Shugaban APC, Jam’iyya Tayi Karin Haske

  • ‘Yan kwamitin NWC na Jam’iyyar APC sun tabbatar da cewa babu barakar cikin gidan da ake fama da ita a yau
  • Nze Duru yace babu wani sabani da Bola Tinubu ya samu da Abdullahi Adamu a game da kwamitin neman takara
  • Mataimakin sakataren gudanarwan na APC yace shugaban jam’iyya da ‘dan takaran na 2023 na kan shafi daya

FCT, Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC ta kasa watau NWC ya yi watsi da jita-jitar rigima tsakanin su Asiwaju Bola Tinubu da Abdullahi Adamu.

Punch tace rahotanni na yawo cewa shugaban APC na kasa bai ji dadin daukar Simon Lalong da Festus Keyamo a kwamitin neman zama shugaban kasa.

Gwamna Simon Lalong shi ne zai jagoranci kwamitin yakin neman zabe da Bola Tinubu yake yi, Festus Keyamo shi ne kakakin wannan kwamitin yin kamfe.

Kara karanta wannan

Tinubu ne ‘Dan takara Mafi Cancanta, Amma Akwai Abin da Nake Tsoro - Shugaban APC

Labaran da ake ji shi ne ‘dan takarar ya zabi wadannan mutane su jagoranci kamfen da zai yi a 2023, ba tare da ya tuntubi Adamu a matsayin shugaba na kasa ba.

Babu batun sauke Adamu - Musawa

Wannan ya biyo bayan an ji Hanatu Musawa tana watsi da maganar da ake yi na tsige Adamu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da aka yi hira da ita a gidan talabijin, Musawa wanda tana cikin manyan kwamitin yakin zama shugaban kasa tace har gobe sai yadda Adamu yace a NWC.

'Yan APC
Abdullahi Adamu da Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Nze Duru yace NWC a dinke ta ke

Ana haka kuma sai aka ji Nze Duru yana bada sanarwa a yammacin Talata, yace babu sabanin da ke tsakanin shugaban APC na kasa da ‘dan takaran na 2023.

The Nation ta rahoto Duru yana cewa shugabannin APC sun ji dadin dauko Simon Lalong da Festus Keyamo da aka yi a matsayin ‘yan kwamitin neman takara.

Kara karanta wannan

Hotuna: Tinubu, Shettima, Adamu da Jiga-Jigan APC Sun Sa Labule a Abuja bayan Ganawa da Wike

“Babu rigimar da ake yi a kan mukamai. Ba a taba yin wannan ba, kuma jam’iyya da ‘dan takara suna aiki tare.
Yana da muhimmanci in ce mun yarda da nadin shugaban kwamitin yakin neman zabe da kakakin kamfe.”
“Gwamnoni za su rike shugabanci a yankunansu. Ba za ayi watsi da jam’iyya ko wani ba, za ayi kamfe da kowa.”

Mataimakin sakataren gudanarwan na APC yake cewa nan gaba kadan jam’iyyarsu za ta sanar da hukumar INEC sunayen ‘yan kwamitin da za su yi wa Tinubu kamfe.

Dalilin tashin Shekarau daga NNPP

Dazu aka ji labari Rabiu Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya jawo NNPP ta rasa Ibrahim Shekarau, duk an ba shi takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a 2023.

Ba a je ko ina ba, tsohon Gwamnan Kano watau Ibrahim Shekarau ya saki tafiyar Rabiu Kwankwaso, sai ya shiga jirgin Atiku Abubakar mai takara a PDP.

Kara karanta wannan

Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel