Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja

Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja

  • Tsohon gwamnan Legas kuma ɗan takarar shugaban kasa na APC ya gana da shugaban APC da jiga-jigai a Abuja
  • Bola Tinubu da Shettima sun gana da jagororin APC ne biyo bayan taron da ya gudana a Landan tare da gwamna Wike na PDP
  • Ibrahim Masari, na hannun dama Tinubu ya yi ikirarin cewa shawo kan Wike kuma zai musu aiki a 2023

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sanata Kasshim Shettima, sun yi wata ganawa ta dabaru da wasu jiga-jigan jam'iyya a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, na daga cikin mahalarta taron tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Ya Sa Labule da Gwamna Wike da Wasu Gwamnoni Uku a Landan

Taron wanda ya guda a Ofishin Kamfe kuma a sirrin ce, ya samu halartar mataimakin shugaban APC na shiyyar kudu maso yamma, Isaac Kekemeke, da shugaban matasa na ƙasa, Dayo Israel.

Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban jam'iyya na shiyyar arewa, Sanata Abubakar Kyari da wasu manyan jiga-jigai a kwmaitin gudanarwa NWC na ƙasa.

Hotunan wurin taro

Bola Tinubu da jiga-jigan APC.
Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja Hoto: Tinubu Support Group/facebook
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Taro ln APC a Abuja.
Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja Hoto: Tinubu Support Group/facebook
Asali: Facebook

Taron APC a Abuja.
Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Me suka tattauna a wurin taron?

Punch ta tattaro cewa duk da ba'a bayyana maƙasudin taron ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoton amma wata majiya ta ce mai yuwuwa taron na da alaƙa da zawarcin gwamna Nyesom Wike da rarrashin mambobin da suka fusata.

Tinubu, wanda ke cigaba dabkokarin shawo kan gwamna Wike game da kudirinsa na maye gurbin shugaba Buhari a 2023, ya gana da gwamnan a Landan ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Atiku ya kade: Obasanjo ya gana da Peter Obi, Wike da wasu jiga-jigai a Landan

Kwanaki biyu bayan haka, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya garzaya ya zauna da Wike a wani yunkuri da ake kallon zai murkushe duk wasu kalaman da Tinubu ya fara jawo hankalinshi da su.

A wani labarin kuma Bayan Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin PDP, Na Hannun Daman Gwamna Ya Sauya Sheka Zuwa APC

Darakta Janar na kungiyar masoyan gwamna Nyesom Wike ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Hakan ta faru ne yayin da wasu bayanai suka nuna Wike da wasu gwamnonin PDP sun sa labule da Bola Tinubu a Landan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel