Kwankwaso Ya Bude Baki Kan Gaskiyar Abin da Ya Faru Da Su da Shekarau a NNPP

Kwankwaso Ya Bude Baki Kan Gaskiyar Abin da Ya Faru Da Su da Shekarau a NNPP

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya jawo Sanata Ibrahim Shekarau ya bar NNPP bayan watanni uku kacal
  • ‘Dan takarar shugaban kasar yace rashin isasshen lokaci ya sa Shekarau ke korafin ba ayi adalci wajen kason takara ba
  • Sanata Kwankwaso ya tabo batun sauya-sheka ganin cewa ya yi tsalle daga PDP da APC tsakanin shekarar 2014 zuwa yau

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - An yi hira da Rabiu Musa Kwankwaso a VOA Hausa inda ya yi bayanin abin da ya jawo Ibrahim Shekarau ya bar NNPP da sunan ba ayi masa adalci ba.

Mai neman takarar shugaban kasar a NNPP ya bayyana cewa kurewar lokaci ya hana a ba ‘yan bangaren Sanata Shekarau takarar kujeru da-dama a jam’iyyarsu.

“Ba mu zauna mun yi dogon zance a kan wannan ba, amma na ga irin sanarwar da wasu suka badawa na cewa ba a ba shi abin da ya dace ko aka yi alkawari ba.

Amma ni na sani, idan aka hadu irin wannan, kowa zai kawo gudumuwa, idan kuma an samu nasara, sai ayi da kowa." - Rabiu Musa Kwankwaso.

Lokaci ya kure mana - Kwankwaso

Kamar yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya fada dazu, abin takaicin shi ne Ibrahim Shekarau bai karasa shigowa cikinsu da kyau ba, lokacin tsaida ‘yan takara ya kure.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwankwaso ya shaidawa ‘yan jaridar a hirar da aka yi da shi cewa kashegarin bada sunayen ‘yan takara Shekarau ya karbi katin NNPP, daga nan duk suka bar Kano.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Buba Galadima Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

‘Dan takaran yace dauko wadanda za a ba ‘yan takara yana da wahala saboda yadda har ta kai akwai kujerar da mutane 17 suka fito, suka nuna sha’awar tikiti.

A cewar Kwankwaso, abin da aka yanke shi ne a duba gaba, ma’ana wajen kafa gwamnati a Kano ko a kasa, ta yadda za a tafi da ragowar mabiyan Sanatan.

Tsohon gwamnan yace zai yi wahala bayan gabatarwa INEC sunaye, a shawo kan 'dan takara ya sauka, don haka aka sa kwamiti da zai duba bukatun Shekarau.

Sauya-sheka a siyasa

A wannan hira da VOA, Sanata Kwankwaso ya yi magana a game da abin da ya sa shi karon kansa ya sauya-shekar siyasa daga jam’iyyun APC da PDP zuwa NNPP.

Fitaccen ‘dan siyasar yace akidunsa sun sha bam-bam da na manyan jam’iyyu, a lokacin da yake sha’awar taimakawa talakawa, yace wasunsa ta kansu suke yi.

Irin rikicin cikin gidan da Kwankwaso ya gani tun 2003 ta sa ya bar PDP a 2014 da tunanin APC za ta kawo mafita, yace a nan ma sai aka ci karo da wasu matsalolin.

Zaben 2023: Tinubu ya dace - Lukman

Dazu kun ji labari Salihu Lukman yana ganin ko Peter Obi, Atiku Abubakar da Rabiu Kwankwaso sun cancanta, Bola Tinubu ya fi su dacewa ya karbi shugabanci.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC na Arewa maso yamma, ya jero abubuwan da suka sa ‘dan takaransu na zaben shugaban kasa ya yi zarra a kan wasunsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel