Kwankwaso: Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba Kuma Ban Tura Mataimaki Na Ya Wakilci Ni Ba

Kwankwaso: Dalilin Da Yasa Ban Halarci Taron NBA Ba Kuma Ban Tura Mataimaki Na Ya Wakilci Ni Ba

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na NNPP ya bayyana dalilin da yasa bai halarci taron NBA ba
  • Kwankwaso, cikin wasikar da ya tura wa shugaban NBA na kasa ya ce wasu muhimman ayyuka da suka shafi kasa ne suka hana shi zuwa
  • Tsohon gwamnan na Jihar Kano kuma ya ce abokin takararsa, Bishop Isaac Idahosa ya tafi kasar waje shi yasa bai tura shi ya wakilce shi ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana dalilin da yasa bai halarci bikin bude taron kungiyar lauyoyi na Najeriya, NBA, na 2022 da aka yi a Legas ba.

Rahotanni sun nuna cewa dan takarar APC, Bola Tinubu da Kwankwaso ba su halarci taron ba duk da cewa yan takarar shugaban kasa na manyan jami'iyyu a kasar sun hallarci taron da aka yi a Legas.

Kara karanta wannan

Taron NBA: Abin da Atiku, Obi suka fada, yayin da aka nemi Kwankwaso aka rasa

Wasikar Kwankwaso ga NBA.
Kwankwaso: Dalilin Da Yasa Ban Hallarci Taron NBA Ba Da Aka Yi A Legas. Hoto: @AbdulAbmJ.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku Abubakar na PDP, Adewole Adebayo na SDP, Peter Obi na LP da Dumebi Kachikwu na ADP suna cikin wadanda suka hallarci taron.

Sai dai Mista Tinubu na APC ya tura abokin takararsa, Kashim Shettima ya wakilce shi.

Dalilin da Kwankwaso ya bada

Amma, dan takarar na NNPP, cikin wasikar bada hakuri da ya tura wa shugaban NBA, Olumide Akpata, ya ce bai samu halartar taron ba saboda wasu muhimman ayyuka na kasa.

Mista Kwankwaso ya ce duk da hakan ya kamata ya tura abokin takararsa, Isaac Idahosa, ya wakilce shi don fada wa kasa tsarin da suka tanada amma ya yi tafiya kasar waje.

Wasikar, wacce kakakin yakin neman zaben Kwankwaso, Abdulmumin Jibrin ya fitar a shafinsa na Twitter ta ce:

"Na rubuta don amsa cewa ya samu wasikar ka kuma ina son sanar da kai cewa ba zan samu halartar wannan taron mai muhimmanci ba sakamakon wasu ayyukan kasa masu muhimmanci.

Kara karanta wannan

Salon Shigar Kashim Shettima Zuwa Taron NBA Ya Dauka Hankulan Jama'a

"A irin wannan yanayin, ya kamata in tura abokin takara na, Bishop Isaac Idahosa, ya wakilce ni don sanar da kasa tsarin cigaba da muka tanada. Amma, ya tafi kasar waje a halin yanzu.
"Don haka, ina son bada hakuri kan rashin samun damar halartar taron kuma ina tabbatar maka NNPP tana tare da NBA a yunkurin samar da zaman lafiya, hadin kai da cigaban kasarmu."

2023: Kwankwaso Ya Kai Wa Babban Sarkin Arewa Ziyara Don Neman Albarka

A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a ranar Juma'a ya ziyarci Ilorin, Jihar Kwara don neman albarka daga Sarkin Ilorin, Alh Ibrahim Sulu-Gambari, kan takarar shugabancin kasa, rahoton Leadership.

Farfesa Shuaib AbdulRaheem dan takarar gwamnan Kwara na NNPP da Dr Kolo Baba Jiya, dan takarar sanata na Kwara North da Alh Buba Galadima ne suka yi wa Kwankwaso rakiya zuwa fadar sarkin.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya Jero Abubuwan da za su Hana Atiku Abubakar Samun Nasara a 2023

Da ya ke jawabi a fadar sarkin bayan sallar Juma'a tare da Sarkin, Kwankwaso ya ce ya taho ilorin ne domin neman albarka daga sarkin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel