Tsohon Gwamnan Kano Shekarau Ya Fita Daga NNPP, Ana Kyautata Zaton Zai Koma APC

Tsohon Gwamnan Kano Shekarau Ya Fita Daga NNPP, Ana Kyautata Zaton Zai Koma APC

  • Bayan mallakar tikitin takarar sanatan Kano ta tsakiya ajam'iyyar NNPP, Shekarau ya raba hanya da tafiyar kayan marmari
  • Kwankwaso ya jawo Shekarau jam'iyyar NNPP, amma wata matsala ta cikin gida ta faru sun raba hanya
  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da shirin 2023, domin tunkarar babban zaben da za a yi kasar nan ba da jimawa ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - A yau Lahadi 22 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya yi sallama da jam'iyyar Kwankwaso NNPP.

Shekarau, wanda sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya ya shiga jam'iyyar NNPP ne waran Mayun wannan shekarar.

Shekarau ya hakura, ya bar NNPP
Tsohon gwamnan Kano Shekarau ya fita daga NNPP, ana kyautata zaton zai joma PDP | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shekarau ya ce ya yi sallama da NNPP ne saboda jam'iyyar ta gaza ba mabiyansa foma-foman cimma burinsu na siyasa a karkashin jam'iyyar.

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, Shekarau ya zargi Kwankwaso da saba alkawarin da suka kulla tun farkon zuwansa NNPP.

Kara karanta wannan

Shekarau ya fito ya yi bayanin dalilan da suka ja ya bar NNPP ya raba gari da Kwankwaso

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake bayyana ficewarsa daga jam'iyyar NNPP, Shekarau ya kalli dandazon masoyansa sannan ya ce:

"Na gama da jam'iyyar NNPP."

Duk da cewa Shekarau bai ayyana wace jam'iyyar zai koma ba, jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mambobin APC da dama sun yi murnar ficewarsa daga NNPP.

A cewar wata majiya daga jam'iyyar APC:

"An shirya Shekarau zai gana da dan takarar shugaban kasan APC, Sanata Ahmad Bola Tunubu, wanda ke son dawowarsa APC, inda ya bari ya koma NNPP asakamakon rasa tikitin takarar sanata a karo na biyu."

Da yaker karin haske game da ficewar tasa da kuma raba hanya da Kwankwaso, Shekarau ya ce NNPP ta ba shi tikin takara amma ta yi biris da dimbin magoya bayansa.

Kwankwaso Mayaudari Ne, Ya Yaudaremu, Inji Tsohon Gwamnan Kano Shekarau

Kara karanta wannan

Kai mayaudari ne: Shekarau ya dira kan Kwankwaso, ya fasa kwai kan maganar sauya sheka

A wani labarin, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yaudare shi da ma magoya bayansa bayan da ya jawo su zuwa jam'iyya mai kayan marmari ta NNPP a watan Mayu.

Shekarau da Kwankwaso dukkansu tsoffin gwamnoni ne a Kano, jiha mafi tashen kasuwanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, Leadership ta ruwaito.

A yau Litinin, 22 ga watan Agusta, Shekarau ya shaida wa manema labarai cewa, zai bayyana matsayinsa na yiwuwar sauya sheka da NNPP zuwa wata jam'iyyar nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel