Dalilin da yasa na fice daga NNPP, na raba kaina da tafiyar Kwankwaso, bayanin Shekarau

Dalilin da yasa na fice daga NNPP, na raba kaina da tafiyar Kwankwaso, bayanin Shekarau

  • Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya bayyana dalilin ficewarsa daga jam'iyyar NNPP
  • Shekarau ya alanta barin NNPP a jiya Litinin 22 ga watan Agusta bayan da ya samu matsala da Kwankwaso
  • Mallam Ibrahim Shekarau ya ce, tabbas Kwankwaso ya yaudare shi, kuma ya yaudari ilahirin magoya bayansa

Jihar Kano - Bayan sauka da motar jam'iyyar NNPP mai alama kayan marmari, Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilan da suka sa yi watsi da jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Sheakau dai shi ne sanata mai wakiltar Kano tsakiya a majalisar dattawa, kuma ya fice daga APC bayan rasa tikitin komawa takara, inda ya koma NNPP aka bashi tikitin.

Shekarau ya bayyana cewa, yanke fice daga NNPP ne biyo bayan hana magoya bayansa foma-fomai tsayawa takara a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Salon Shigar Kashim Shettima Zuwa Taron NBA Ya Dauka Hankulan Jama'a

Dalilai da suka sa Shekarau ya fusata, ya bar NNPP
Dalilin da yasa na fice daga NNPP, na raba kaina da tafiyar Kwankwaso, bayanin Shekarau | Hoto: dailytust.com
Asali: Twitter

Da damu da yadda aka yi watsi da magoya bayana

Da yake bayyana abin da ya faru tsakaninsa da Kwankwaso, Sheakarau ya ce ransa ya yi matukar baci ganin yadda aka yi watsi da magoya bayansa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shekarau ya ce, kafin shigowarsa NNPP, ya zauna da Kwankwaso a gida, sun tattauna matuka game da makomar siyasarsu da kuma tafiyar NNPP.

Ya ce Kwankwaso ya ji dadi sosai da wannan shawara, kuma daga karshe dai ya shigo jam'iyyar NNPP, Vanguard ta ruwaito.

Shekarau ya kuma ce ya nemi ba da sunayen magoya bayansa ga Kwankwaso, amma basu samu damar ganawa ba kasancewar tun haduwarsu ta farko ranar 5 ga watan Mayu basu sake haduwa ba har 11 ga watan.

Ya kara da cewa:

“Takardar na dauke da jerin sunayen magoya bayana da ke neman kujeru mabambanta na siyasa, sadda na yiwa Kwankwaso magana kai ya ce yana sane da su kuma tabbas za a yi wani abu akai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Shekarau ya raba hanya da Kwankwaso, ya fice daga NNPP

“Hakazalika, ranar 16 ga Mayu, 2022, Kwankwaso ya zo kusan karfe 9 na dare har ila yau muka tattauna wadancan batutuwan. Ya ma kira mutane biyar ciki har da Abba Kabir da Kawu Sumaila da Alhassan Rirum da wasu mutum biyu ya ce ne wadanda za su hada jerin sunayen ‘yan takara."

Sai dai, Shekarau ya ce Kwankwaso da kansa ya kawo fom din sanata ya bashi amma bai kawo na magoya bayansa ko daya ba.

Da ya tambaya, Kwankwaso ya ce zai kawo wanda tun lokacin a cewar Shekarau ya fara yaudararsa. Wannan yasa ya bar NNPP.

Kwankwaso Mayaudari Ne, Ya Yaudaremu, Inji Tsohon Gwamnan Kano Shekarau

A wani labarin, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda Sanata Rabiu Kwankwaso, ya yaudare shi da ma magoya bayansa bayan da ya jawo su zuwa jam'iyya mai kayan marmari ta NNPP a watan Mayu.

Shekarau da Kwankwaso dukkansu tsoffin gwamnoni ne a Kano, jiha mafi tashen kasuwanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kai mayaudari ne: Shekarau ya dira kan Kwankwaso, ya fasa kwai kan maganar sauya sheka

A yau Litinin, 22 ga watan Agusta, Shekarau ya shaida wa manema labarai cewa, zai bayyana matsayinsa na yiwuwar sauya sheka da NNPP zuwa wata jam'iyyar nan ba da jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel