Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

  • Ana tunanin cewa tauraruwar Shugaba Muhammadu Buhari ta fara dushewa a siyasar Najeriya
  • Domin wasu na-kusa da Shugaban kasar sun nemi kujeru a APC, sai ga shi ba su iya samun tikiti ba
  • A cikin wadanda suka sha kashi a zaben fitar da gwani na APC har da ‘danuwan shugaban kasar

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jaridar nan ta Premium Times ta tattaro sunayen ‘yanuwa da tsofaffin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari da suka rasa zaben fitar da gwani.

Legit.ng ta bibiyi jerin, ta kuma kara da na ta bayanin a wannan rahoto:

1. Fatuhu Mustapha

Muhammadu Buhari uba yake ga Fatihu Muhammad, amma alakar nan ba tayi amfani wajen tsaida ‘dan takarar APC na shiyyar Daura/Sandamu/Maiadua ba.

Aminu Jamu ne zai yi wa yankin takarar ‘dan majalisar wakilan tarayya. Hon. Muhammad wanda shi yake rike da kujerar ya samu kuri’a 30, Jamu na da 117.

2. Sha’aban Ibrahim Sharada

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada mai wakiltar birnin Kano a majalisar wakilan tarayya ya nemi tikitin takarar gwamnan jihar Kano a karkashin APC mai mulki.

Sharada ya sha kashi a hannun Nasiru Yusuf Gawuna duk shi tsohon hadimin shugaban kasa ne. Matashin yana tare da Buhari tun a ANPP, CPC har zuwa APC.

3. Ismaeel Ahmed

Ismaeel Ahmed ya rike mukamin mai taimakawa a fadar shugaban kasa. Ahmed ya yi sha’awar zama Sanatan Kano ta tsakiya a APC, amma a karshe ya hakura.

Buhari
Sha'aban Sharada APC tare da Shugaban kasa Buhari Hoto: kanofocus.com
Asali: UGC

Tsohon hadimin shugaban kasar ya janye takararsa bayan Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya lallabesa. A. A Zaura ne wanda ya samu tikitin APC.

4. Bashir Ahmad

Bashir Ahmaad ya yi yunkurin wakiltar mutanen Gaya/Ajingi/Albasu a majalisar wakilan tarayya. Shi ma matashin bai iya lashe zaben fitar da gwani ba.

Ahmaad yana cikin tsirararun matasan da ke cikin gwamnatin Muhammadu Buhari, da kuri’u 16 rak ya sha a zaben da aka ji labarin yana cewa an yi magudi.

5. Sani Sha’aban

Muhammad Sani Shaaban Suruki ne ga shugaban Najeriya, shi ma bai samu tikitin gwamna a jam’iyyar APC ba duk da ‘dan sa ya yi aure daga fadar Aso Villa.

Hon. Sani Shaaban wanda ya nemi zama ‘dan takarar gwamnan Kaduna ya zo na uku ne a zaben inda ya samu kuri’u 20 yayin da Sanata Uba Sani ya tashi da 1,149.

6. Ita Enang

Sanata Ita Enang ya ajiye aikinsa a fadar shugaban kasa da nufin ya zama ‘dan takarar gwamnan Akwa Ibom, a karshe Obong Akanimo Udofia ne aka tsaida a APC.

Tsohon 'dan majalisar kuma Mai bada shawara ga shugaban kasa a kan harkokin Neja-Delta, ya lale Naira miliyan 50, ya saye fam, takararsa ba ta kai ko ina ba.

7. Faruk Adamu Aliyu

Hon. Faruk Ádámù Aliyu da bakinsa ya amsa cewa yana cikin manyan na kusa da shugaban kasa, duk da kuwa bai da wani mukami a rubuce a gwamnatin tarayya.

Tsohon ‘dan majalisar ya nemi APC ta tsaida shi a matsayin ‘dan takaran gwamnan Jigawa, amma kuri’a 15 ya ci a zaben tsaida gwani, Umar Namadi aka tsaida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel