2023: Bayan Atiku, Tinubu Shima Yana Zawarcin Shekarau, Za Su Gana Ranar Laraba

2023: Bayan Atiku, Tinubu Shima Yana Zawarcin Shekarau, Za Su Gana Ranar Laraba

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC zai gana da Sanata Ibrahim Shekarau a ranar Laraba
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ana kyautata zaton tsohon gwamnan na Jihar Legas din zai gana da Shekarau ne da nufin zawarcinsa ya dawo APC
  • A baya-bayan nan rahotanni sun nuna cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP shima ya yi wa Shekarau tayin mukami idan zai dawo PDP

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya gayyaci tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zuwa taro a ranar Laraba, kwararan majiyoyi suka shaidawa Daily Nigerian.

Dan takarar shugaban kasar na APC ya gayyaci Mista Shekarau, wanda shine dan takarar sanata na jam'iyyar NNPP, zuwa taro domin zawarcinsa ya dawo jam'iyyarsa.

Kara karanta wannan

Yan Majalisu Biyu Da Dubbannin Yan Siyasa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Gangamin Atiku

Shekarau da Tinubu
Shekarau Zai Gana Da Tinubu A Ranar Laraba A Yayin APC Da PDP Ke Zawarcin Tsohon Gwamnan. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Twitter

Daily Nigerian ta rahoto cewa Mista Shekarau ya riga ya cimma yarjejeniya da dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar cewa zai koma jam'iyyarsu a nada shi shugaban kamfen na Arewa maso Yamma.

Sai dai mai magana da yawun Shekarau, Bello Sharada ya musanta wannan rahoton yana mai cewa an tattauna batun wurin taron Shura amma ba a amincewa da komawar Malam zuwa PDP ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban jigo a jam'iyyar PDP a Kano ya shaidawa Daily Nigerian cewa jam'iyyar ta fara shirin sauya tsare-tsarenta don maraba da Shekarau.

A cewarsa, mataimakin shuganan PDP na yankin arewa maso yamma, Bello Hayatu Gwarzo, ya sanar da manyan shugabannin jam'iyyar game da zuwan Shekarau da shirin tarbarsa.

Daily Nigerian ta samu sahihin rahoto cewa abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima, da farko ya gana da Shekarau a ranar 8 ga watan Agusta amma majiyoyi sun ce "ba dai-daita ba".

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bangaren Shekarau Ta Magantu Kan Jita-Jitar Komawarsa PDP

Duk da cewa wasu na kusa da tsohon gwamnan sun ce ya riga ya yanke shawarar komawa PDP, shi (Shekarau) - saboda 'ganin ido' - ya kira taron masu bashi shawara, kwamitin Shura, don su basu shawara.

Ana sa ran kwamitin za ta kammala rahotonta yau sannan a sanar da matakin da ta dauka a makon mai zuwa.

Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ta Kwankwaso Ya Koma PDP Saboda Wasu Alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa

Tunda farko, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau zai sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa PDP biyo bayan wani alƙawari 'mai tsoka' da aka ce dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya masa.

Mista Shekarau, wanda ke wakiltar Kano Central, ya sanar da ficewarsa a hukumance daga APC zuwa NNPP cikin wata wasika da shugaban majalisa, Lawan Ahmad ya karanto a ranar 29 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel