Tinubu Zai Fuskanci Matsala Tun Yanzu, Ana Hure Kunnen Darektan Kamfen da Ya Zaba

Tinubu Zai Fuskanci Matsala Tun Yanzu, Ana Hure Kunnen Darektan Kamfen da Ya Zaba

  • ‘Yan North Central APC Forum ba su goyon bayan Simon Bako Lalong ya zama shugaban kamfe
  • Kungiyar ta fadawa Gwamnan na jihar Filato cewa ka da ya karbi tayin DG domin sun fi karfin kujerar
  • Saleh Mandung Zazzaga yace ‘yan yankin na harin Shugaban kasa ko mataimakisa ne

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Plateau - Wasu jagorori da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a karkashin inuwar North Central APC Forum sun raina mukamin da aka ba Simon Bako Lalong.

This Day tace shugaban North Central APC Forum ya fitar da wani jawabi, yana kira ga Gwamnan na Filato ya yi watsi da tayin da aka yi masa.

Gwamna Simon Bako Lalong aka zaba a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Shettima, hakan bai yi wa kungiyar dadi ba.

Kara karanta wannan

A Dena Kawo Addini Cikin Siyasa, In Ji Lalong, Shugaban Yakin Neman Zaben Tinubu

Saleh Mandung Zazzaga yace abin da suke nema a 2023 shi ne shugaban kasa ya fito daga yankinsu, a karshe dai ba su samu takarar a 2023 ba.

Harin Aso Villa tun 1999

A jawabin da Zazzaga ya aikawa jaridar, ya nuna ba Darekta Janar na kamfe suke nema ba domin babu ‘dan yakin da ya taba shiga Aso Villa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tun bayan mulkin soja, ba a taba samun ‘dan siyasa daga yankin Arewa maso tsakiya ya dare kujerar shugaban kasa ko mataimakinsa ba.

Manyan APC
Shettima, Adamu, Buhari, Tinubu, Lalong Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Zazzaga yace daga baya sun hakura da neman shugaban kasa saboda APC ta kai takararta kudu, da tunanin za su fito da abokin tafiyar Tinubu.

A nan ma Arewa maso tsakiya ba ta dace ba, aka zakulo ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyya mai mulki daga Arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

2023: Ana Kokarin Kawo Karshen Rikicin Jam’iyyar PDP, Atiku Ya Zauna da Wike

Jawabin Saleh Mandung Zazzaga

“Idan jam’iyyar ta na gani babu wani daga Arewa ta tsakiya da ya dace ya shiga takarar shugaban kasa saboda babu wanda zai iya tattaro kuri’un Arewa, ya aka yi jam’iyyar ko Tinubu suka yarda da ‘dan yankin ya zama Darekta Janar na kwamitin kamfe?
“Abin da muka nema a zaben 2023 shi ne ko mu fito da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa, amma aka hana mu saboda ana tunanin ba mu dace ba, ko bamu da mu da karfi. Da aka zo neman Darektan kamfe, kwatsam sai aka ga mun cancanta.”

Mun fi karfin DG - Zazzaga

Daily Trust ta rahoto shugaban na North Central APC Forum yana cewa tun farko Simon Lalong suka so ya zama ‘dan takarar shugaban kasa ko mataimaki.

Kungiyar tace an raina yankin na su da aka ba su wannan kujera, kuma ba za su karba ba, a karshe suka yi kira ga Lalong cewa ka da ya karbi tayin na APC.

Kara karanta wannan

Oshiomhole Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Wa Magoya Bayan Peter Obi Idan Suka Ce Za Su Tanka Masa

Lauya ya je kotu

Dazu labari ya zo cewa wani kauya ya kinkimo aiki, ya roki Alkali ya umarci hukumar INEC ta fito da takardun da Bola Tinubu ya gabatar na shiga zabe.

Barista Mike Enahoro-Ebah ya maka INEC a kotun tarayya ne saboda ya nemi fam din ‘Dan takaran APC ya cike, amma an hana shi, wanda hakan ya saba doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel