Dalibin Makarantar Sakandare Ya Kera Na'urar Mutum Mutumi Da Kansa A Jihar Kano

Dalibin Makarantar Sakandare Ya Kera Na'urar Mutum Mutumi Da Kansa A Jihar Kano

  • Wani Dalibi mai suna Isah Barde, da ya kammala karatunsa na sakandare a jihar Kano, ya kera Na'urar Mutum Mutumi daga tarkace
  • Isah Barde ya ce burin sa shine ya zama kwararre a harkar leken asiri da kuma injiniya mai Fasahar kere-kere
  • Mahaifin Isah, Auwal Barde, yana alfahari da babban injiniyan dake gidan sa, amma ba shi da kudin da zai taimaka wa Isah ya cika burinsa

Jihar Kano - Isah Barde, matashi dan shekara 17 da ya kammala karatunsa na sakandare a jihar Kano, ya kera Na'urar Mutum Mutumi daga tarkace, inda ya yi amfani da kwali, bututu, ledodi, moto, aluminum, da dai sauransu, a matsayin kayan aikin sa, rahoton Daily Trust

Isah yayi nazarin karantar fasahar kere-kere da zama kwararre a harkar leken asiri, duk da matsalar kudi da ke gabansa.

Kara karanta wannan

Mafi tsufa a raye: An gano wani tsoho dan Najeriya mai shekaru 126 a raye kuma da karfinsa

Shekaru uku kenan da matashin ya fara kera na’urar mutum-mutumi, wanda ya bayyana a matsayin wani bangare na burin rayuwarsa, duk da karancin tallafi.

Yana sarrafa Na'urar Mutum Mutumin din ta hanyar motsa hannayensa.

robot
Dalibin Makarantar Sakandare Ya kera‘Robot’ A Jihar Kano FOTO Daily Trust
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Isah ya shaidawa Trust TV cewa mutum-mutumin an yi shi da kwali, bututu, LED, motor, aluminum, da sauransu.

Isa Barde ya kara da cewa akwai abubuwan da ya samu daga hannun mutane da kuma wata kasuwa mai suna Jakara inda yake iya siyan abubuwa kamar na’urar busar da gashi da ta lalace.

Mahaifin Isah, Auwal Barde, yana alfahari da babban injiniyan dake gidan sa, amma ba shi da kudin da zai taimaka wa Isah ya cika burinsa.

Auwal Barde ya ce bashi da hanyar tallafa masa amma zan yi farin ciki idan ya samu goyon baya a wani wuri ko daga gwamnati ko kuma daidaikun mutane.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

An bayyana cewa Isah ya fara nuna sha’awar aikin injiniya tun yana dan shekara 8, kuma tun daga nan ya jajirce wajen ganin ya inganta fasaharsa.

2023: Shugaban Matasan APC Dayo Israel Ya Fitar Da Bidiyon Tinubu Yana Taro A Karfe Daya Na

A wani labari, A wata ganawa da ya yi da wasu ‘yan Najeriya kwanan nan a birnin Landan, Dayo Isra’ila, shugaban matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai kwanta barci da karfe 4 na safe a rana ta farko.

Da yake raba bidiyon a shafinsa na Instagram, Israel ya ce Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, yana da dakunan guda bakwai a gidansa da kuma yana shiga daya bayan daywa don ganawa da maziyartan sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel