Gwamnan APC ya ba Kiristoci Shawara Tun da APC ta Kinkimo Musulmi da Musulmi a 2023

Gwamnan APC ya ba Kiristoci Shawara Tun da APC ta Kinkimo Musulmi da Musulmi a 2023

  • Kayode Fayemi ya karbi bakuncin shugabannin CAN na Ekiti a karkashin jagorancin Emmanuel Aribasoye
  • Gwamnan jihar Ekiti ya shaidawa kungiyar CAN cewa neman hanyar cin zabe ne ta sa APC ta dauko Musulmai biyu
  • Fayemi ya yi kira ga Kiristoci da su shiga harkar siyasa a rika damawa da su, domin su sha romon damukaradiyya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ekiti - Dr. Kayode Fayemi wanda shi ne Gwamnan jihar Ekiti, ya yi kira ga Kiristocin kasar nan su ajiye batun addini a gefe, su zabi ‘yan takaran APC.

Leadership ta ce Mai girma Gwamnan ya yi wannan kira a lokacin da sababbin shugabannin kungiyar CAN na Ekiti, suka kai masa ziyara a ofishinsa.

Da yake yi wa Dr Emmanuel Aribasoye bayani, Gwamna Kayode Fayemi ya nuna APC ba ta tsaida Musulmi da Musulmi saboda a murkushe kiristoci ba.

Kara karanta wannan

Amaechi: Daliget Da Suka Sayar Da Kuri'unsu Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC Suna Nadama

Kayode Fayemi yake cewa jam’iyyarsu ta dauko wannan salo ne saboda lashe zaben shugaban kasa.

A cewar tsohon Ministan, ya kamata jama’a su cire madubin addini da kabilanci a zaben shugaban kasa na 2023, su nemi yadda za su ci ribar gwamnati.

Shawarar Kayode Fayemi

“Ya kamata a fahimci akwai dalilin da suka tursasawa Kiristoci shiga zabe. A ra’ayina, koyarwar kiristanci zai taimaka mana wajen zama ‘yan kasa nagari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan APC
Gwamna Kayode Fayemi a gidan makoki Hoto: @kfayemi
Asali: Twitter

Shugabannin kiristoci suyi amfani da wannan kalubale a matsayin dama, wajen gabatarwa jam’iyyu musamman ta mu ta APC, da mafi karancin bukatunsu.
Ko da yana da kyau a ga kowane bangare a tikitin shugaban kasa, amma yana da muhimmanci mu yi duba a wajen addininmu, kabila ko inda muka fito."

Ba mu natsu ba - CAN

Shugaban CAN na jihar Ekiti, Dr Emmanuel Aribasoye da ‘yan tawagarsa sun nunawa Gwamnan cewa hankalinsu bai kwanta da abin da APC ta zo da shi ba.

Kara karanta wannan

Na kadu: An kashe dan uwan shugaban PDP, Buhari ya sha alwashin daukar mataki, ya kakkausan martani

Fayemi ya fahimtar da jagororin kiristocin cewa APC ba tayi watsi da kiristocin yankin Arewa saboda babu wanda ya dace ba, kamar yadda wasu suke rayawa.

An rahoto Gwamnan Ekitin yana cewa ko mutum bai gamsu da tikitin Musulmi da Musulmi a takarar kasa ba, ya kamata a fahimci dabarun siyasa ne ba komai ba.

Labari mara dadi

Kun samu rahoto dazu cewa an wayi gari a Sapele da labarin tsintar gawar na-kusa da ‘Dan takarar Gwamnan jihar Delta a karkashin APC, Ovie Omo Agege.

Mataimakin Shugaban Majalisa Dattawan, ya rasa Hadiminsa, Hon. Cyril Makanaki a sakamakon buda masa wuta da 'yan bindiga suka yi a cikin gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel