Da dumi-dumi: Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a Daura

Da dumi-dumi: Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a Daura

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga ganawar sirri tare da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu da gwamnan jihar Katsina
  • Tinubu dai ya isa Daura da ke jihar Kastina a yau Lahadi, 10 ga watan Yuli, domin kaiwa Buhari gaisuwar sallah
  • Nan take kuma sai manyan jiga-jigan na jam'iyyar mai mulki a kasar suka shiga cikin wata ganawa ta sirri

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Katsina - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya isa garin Daura da ke jihar Katsina, jaridar Leadership ta rahoto.

Da isarsa Katsina, Tinubu ya samu tarba daga gwamnan jihar, Aminu Bello Masari da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar a ranar Lahadi, 10 ga watan Yuli.

Tinubu yayin da Tawagar Masari suka tarbe shi a Katsina
Da dumi-dumi: Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a Daura Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Daga nan jiga-jigan jam’iyyar mai mulki biyu suka garzaya zuwa gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin kai masa gaisuwar Sallah.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Buhari, Tinubu da Masari sun shiga ganawar sirri a yanzu haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya dauki Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa

Mun dai ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives (APC) a zaben 2023, Bola Tinubu, ya bayyana abokin takararsa.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Tinubu ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa a babban zaben mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta kuma rahoto cewa a yau Lahadi, 10 ga watan Yuli, za a bayyanawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar na mataimakin shugaban kasa a mahaifarsa ta Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel