Duka bangarorin Arewa su na ta sa-in-sa a kan wanda zai yi wa Tinubu mataimaki a APC

Duka bangarorin Arewa su na ta sa-in-sa a kan wanda zai yi wa Tinubu mataimaki a APC

  • Har yanzu ‘dan takaran shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai tsaida abokin tafiyarsa ba
  • Kungiyoyi su na ta fitowa su na bada shawarar wanda ya kamata Bola Ahmed Tinubu ya dauka a 2023
  • Tsakanin Mutanen yankin Arewa maso yamma da makwabtansu, kowa na ganin shi ne ya fi cancanta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Nigeria - Tsakanin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas da tsakiya, ba a cin ma matsaya a kan wa zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasan APC ba.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ‘yan siyasar wadannan yankuna sun ci burin zama abokan takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a karkashin jam’iyya mai mulki.

Masu ruwa da tsaki a APC su na harin tikitin mataimakin shugaban kasa a zaben da za ayi a 2023.

Kara karanta wannan

Mance da su Ganduje da El-Rufai: Ka zabi abokin takara da Arewa ta tsakiya, jiga-jigan APC ga Tinubu

Arewa maso yamma su na takama da yawan kuri’u, don haka suke cewa idan zabe ake shirin lashewa, ya kamata a tsaida wani daga cikin gwamnonin yankin.

Lokacin Arewa maso tsakiya ne

A karshen wani taro da masu ruwa da tsaki na APC na shiyyar Arewa maso gabas suka yi, mun ji sun nemi a ba ‘yan Arewa ta tsakiya takarar kujera ta biyu a matsayi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar North East APC Stakeholders Coalition ta tashi taron Lahadi da ra’ayin cewa adalci da gaskiya shi ne a tsaida abokin takarar Bola Tinubu daga tsakiyar Arewa.

Bola Tinubu
'Dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Shugaban wannan kungiya, Alhaji Abba Aji Suleiman, ya yi wa makwabtansa na Arewa maso yamma raddi, ya ce ya kamata a 2023, a waiwayi 'Yan Arewa ta tsakiya.

Abba Aji Suleiman yake cewa akwai rashin adalci da son kai idan aka kara maida yankin saniyar ware wajen abubuwan da suka shafi jam’iyya da shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Rabiu Kwankwaso bai cire ran hada-kai da Peter Obi ba, duk da 'Yan hana ruwa gudu

Ba ayi da Arewa ta tsakiya

North East APC Stakeholders Coalition ta ce yankinsa sun hakura da mukamin, su na goyon bayan Arewa maso tsakiya domin ba su taba samun babbar dama ba.

A cikin manyan jam’iyyun siyasa, babu wanda ya tsaida mutumin wannan shiyya a matsayin ‘dan takarar shugabancin kasa ko kuma akalla ‘dan takarar mataimaki.

Arewa maso yamma su na nema

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka ji kungiyar nan ta TSO ta na bada sanarwar cewa Gwamna Nasir El-Rufai ta ke goyon bayan ya zama abokin takarar Bola Tinubu.

'Yan kungiyar Tinubu Support Organization (TSO) sun ce da suka yi bincikensu, sun fahimci wanda ya kamata APC ta ba tikiti a 2023 shi ne gwamnan jihar Kaduna.

Rahotanni na nuna cewa Bola Tinubu ya fi karkata ne zuwa ga 'yan siyasar Arewa maso yamma. A yankin APC ta na mulki a jihohi uku, PDP ma ta na rike da jihohi uku.

Kara karanta wannan

2023: An Bayyana Sunayen Jiga-Jigan APC 2 Da Tinubu Zai Zabi Mataimakinsa Daga Cikinsu

Asali: Legit.ng

Online view pixel