Kaduna: Kungiyar APC Ta Bayyana Wanda Ya Dace Uba Sani Ya Zaba a Matsayin Mataimakinsa
- Kungiyar magoya bayan APC ta Kudancin Kaduna ta shawarci dan takarar gwamna na jam'iyyar Sanata Uba Sani ya zabi Dr Manzo Daniel Maigari a matsayin mataimakinsa
- Kungiyar ta ce ta yi nazari mai zurfi ta kuma gano cewa babu wani dan siyasa daga kudancin Kaduna da ya bada gudumawa kamar Dr Manzo tun 2015
- Dr Manzo ya rike mukamin tsohon kwamishina na Ma'aikatar Noma da Kasuwanci a karkashin gwamnatin Gwamna Nasir El-Rufai a zango na farko
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kaduna - Kungiyar magoya bayan APC daga kudancin Kaduna, 'The Coalition of Southern Kaduna All Progressives Congress Volunteer Group' ta sha alwashin yin aiki don ganin nasarar Sanata Uba Sani a matsayin gwamna a zaben 2023.
Kungiyar ta kuma goyi bayan a zabi tsohon kwamishinan Noma, Dr Manzo Daniel Maigari, a matsayin wanda ya dace ya yi wa Sani mataimaki, rahoton The Punch.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Maigari tsohon kwamishinan Noma da Kasuwanci ne a karkashin zangon farko na mulkin Gwamna Nasir El-Rufai a jihar.
Shugaban kungiyar, Abeku Audu, cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce sun goyi bayan zaben tsohon kwamishinan ne bayan nazari mai zurfi kan halayensa.
Ya ce tun bayan kafuwar gwamnatin APC a Kaduna a 2015, babu wani dan siyasa daga kudancin Kaduna da ya bada gudunmawa da kuma ya yi fice kamar Dr Manzo.
Wani sashi na sanarwar ta ce:
"Mun zabi Dr Manzo ne a matsayin a dan takarar mataimakin gwamna bayan nazari mai zurfi kan halayen mutumin da ya jagoranci ma'aikatu biyu ya kuma samu nasarori masu yawa.
"Tun bayan kafuwar gwamnatin APC a Kaduna a 2015, babu wani dan siyasa daga kudancin Kaduna da ya yi fice kuma ya bada gudunmawa kamar Dr Manzo."
Dr Manzo ya yi karatu a kasashen duniya kamar Netherland, Singapore, Switzerland da sauransu a cewar kungiyar.
Mai neman takarar kujerar majalisar dokoki ta Jihar Kaduna a APC ya magantu kan batun zaben mataimakin Uba Sani
A game da batun zaben wanda zai yi wa Uba Sani mataimaki a zaben na 2023 da ke tafe, Legit Hausa ta samu ji ta bakin Mallam Muhammad Rili, Mai neman tikitin takarar dan majalisar dokoki ta Jihar Kaduna, mazabar Ikara a karkashin jam'iyyar APC.
Ra'ayinsa ya sha bam-bam da na kungiyar ta kudancin Kaduna da ke neman ganin Uba Sani ya dauki Dr Manzo a matsayin mataimakinsa.
Rili ya ce kamata ya yi APC ta zabo mataimakin Uba Sani daga Zone 1, duba da cewa wannan yankin ne jam'iyyar ta fi karfi kuma dan takarar gwamna na PDP shima daga Zone 1 ya fito, yayin da shi kuma Uba Sani ya fito ne daga Zone II.
"Bana goyon baya saboda Zone 1 ne yankin da APC ta fi karfi a Jihar Kaduna kuma duba da cewa dan takarar gwamna na PDP shima dan Zone 1 ne, jam'iyyar ba za ta iya sakaci da yankin da ta fi karfi ba.
"Don haka, ni ina goyon bayan jam'iyyar APC ta zabo mataimakin gwamna daga Zone 1. (Mazabar Kaduna ta Arewa)," in ji shi.
Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen
A wani rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.
Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.
Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.
Asali: Legit.ng