Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nuna Sanata Kashim Shettima yake so su yi takara tare a zaben 2023
  • Amb. Babagana Kingibe da Janar Aliyu Gusau sun fitar da mutane 6 da APC da PDP za su zaba
  • Ana tunanin wanda zai zama abokin takarar Atiku Abubakar wannan karo shi ne Ifeanyi Okowa

AbujaDaily Trust ta ce mutanen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da na Atiku Abubakar sun tsuke neman abokin takararsu zuwa ga mutane biyu a halin yanzu.

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima ake tunanin Bola Ahmed Tinubu zai zaba su yi takara a tare.

Rahoton da aka fitar dazu ya bayyana cewa ‘dan takaran na APC ya bada sunan tsohon gwamnan na jihar Borno a matsayin wanda zai yi masa mataimaki a 2023.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen tsoffin masu takara da Tinubu ya ziyarta tun bayan da ya mallaki tutar APC

Sanatan na tsakiyar Borno ya taka rawar gani wajen taya Bola Tinubu neman tikitin shugaban kasa a jam’iyyar APC, kuma ya fito daga yankin Arewa maso gabas.

Meyasa Tinubu yake son Shettima?

Kamar yadda majiyar ta bayyanawa jaridar, Tinubu ya gamsu da Sanata Shettima saboda goyon bayansa da ya yi, kuma ya na ganin zai samu karbuwa a ko ina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana tunanin tsohon gwamnan ya na da mutane a fadin kasar nan. Shettima ya rike shugaban gwamnonin Arewa, kuma yanzu haka ‘dan majaliar dattawa ne.

Tinubu
Tinubu, Kashim da Zulum Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC

Inda Shettima ya sha gaban sauran wadanda ake tunani shi ne duka gwamnoni uku da APC ta ke da shi a bangaren Arewa maso gabas su na tare da shi a siyasa.

Babagana Zulum, Mai Mala Buni da Muhammed Inuwa Yahaya duk su na da alaka mai kyau da shi, kuma Zulum ba ya nuna bai sha’awar takara a zabe na kasa.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

Inda matsalar ta ke

Ambasada Babagana Kingibe ya ba Gwamna Atiku Bagudu sunayen mutane uku ne; Babagana Umara Zulum; Amina J. Mohammed da Kashim Ibrahim-Imam.

Su kuma ‘yan bangaren CPC a tafiyar APC su na goyon bayan daya daga cikin Ministocin tarayya, Abubakar Malami ko Sanata Hadi Sirika ya samu wuri a tikitin.

Amma an ce Mai girma Shugaba Muhammadu Buhari bai da wata matsala da Sanatan na Borno.

Kwamishinan harkar ilmi na jihar Bauchi, Dr. Aliyu U. Tilde ya kyankyasa mutane a shafinsa na Facebook cewa akwai yiwuwar Shettima za a dauka a APC.

Dr. Ifeanyi Okowa da Atiku Abubakar

A jam’iyyar PDP kuwa, kusan an tsaida magana ne a kan Gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa.

Idan abubuwa ba su sake zani ba, babu mamaki Ifeanyi Okowa zai zama abokin takarar Atiku Abubakar Abubakar a zabe mai zuwa a karkashin jam’iyyar PDP.

Janar Aliyu Gusau da ‘yan kwamitinsa sun ba Atiku shawarar ya dauki Sanata Okowa ko kuma - Nyesom Wike da Udom Emmanuel , idan hakan ba za ta samu ba.

Kara karanta wannan

Ba sauran hamayya: Yahaya Bello ya ba da tallafi mai tsoka ga ci gaban kamfen din Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel