Mata sun karbe Gwamnatin Kaduna a hannun maza, su ke da rijanyen Kwamishinoni

Mata sun karbe Gwamnatin Kaduna a hannun maza, su ke da rijanyen Kwamishinoni

  • Mataimakiyar Gwamnan Kaduna ta rantsar da wadanda Gwamna Nasir El-Rufai ya ba mukamai
  • A wajen rantsarwar, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta ce adadin mata ya zarce na maza yawa a majalisar SEC
  • Yanzu akwai mata 9 a kan kujerar Kwamishina a jihar Kaduna, maza kuwa su na da kwamishinoni 8

Kaduna - Adadin matan da suke kan kujerar kwamishinoni a jihar Kaduna ya zarce na maza a halin yanzu. The Cable ta fitar da wannan rahoto a makon nan.

Mataimakiyar Gwamnan Kaduna, Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta bayyana cewa a cikin kwamishinoni 17 da ake da su a yau, mata su ke da kashi 53%.

A majalisar zartarwa ta jihar Kaduna akwai kwamishinoni mata tara, sai kuma maza takwas.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta jinjinawa Mai girma Nasir El-Rufai a sa’ilin da ta ke rantsar da sababbin wadanda aka rabawa mukamai a ranar Larabar nan.

Mataimakiyar gwamnan ta ke cewa babu inda mata su ke jin dadi a gwamnati irin Kaduna. A cewar ta, gwamnatin Kaduna tayi zarra a wannan babi a Afrika.

Gwamnatin Kaduna
Hadiza Sabuwa Balarabe da Umma K. Ahmed Hoto: @insidekaduna
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mata sun samu babbar ma'aikata

“Babu tantama adadin matan da ke rike da mukaman kwamishina a Kaduna, yana cikin na inda suka fi ko ina yawa a Afrika, kuma na farko a Najeriya.”
“Wannan ne karon farko da mace za ta rike ma’aikatar kananan hukumomomi a matsayin Kwamishina a tarihi. A da, maza ne aka warewa kujerar.”
“Nasir El-Rufai ne kurum zai iya saba abin da ake dade ana yi wanda ya hana kawo cigaba, kamar mallakawa maza ma’aikatar kananan hukumomi.”

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Daily Trust ta ce Umma K. Ahmed aka rantsar a matsayin Kwamishinar harkar kananan hukumomi.

Sauran wadanda aka rantsar a jiya sun hada da Rt. Hon. Aminu Abdullahi Shagali PhD, ya zama Mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara a kan harkokin siyasa.

Dr. Yusuf Yakubu Arrigasiyyu ya zama sabon shugaban hukumar kula da mahajjata. Wannan karo hukumar za ta kula da sha’anin Kiristoci da Musulman jihar.

ASUU da Gwamnan Edo

Saboda malaman jami’a sun shiga yajin-aiki, sai aka ji labarin Gwamnan Edo ya dakatar da ‘Yan ASUU, ya hana su albashinsu, sannan duk ya kore su daga aiki.

Yanzu haka Gwamnati ta na barazanar za ta dauki sababbin Malaman Jami’a a Edo. Wannan ya sa ASUU ta shigar da kara a kotun ma'aikata da ke garin Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel