Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

  • Muddin abubuwa suka cigaba da tafiya a halin da ake ciki, to babu kirista a tikitin jam'iyyar APC
  • Kashim Shettima shi ne wanda aka fi tunanin zai zama abokin takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • An fi tunanin dauko tsohon Gwamnan jihar Borno a kan a dauki wani Kirista daga yankin Arewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Idan ba an samu wasu canji a gab da karshen lokaci ba, Sanata Kashim Shettima ne zai zama abokin takarar Asiwaju Bola Tinubu a zaben 2023.

Vanguard ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 16 ga watan Yuni 2022 da ya tabbatar da cewa sunan Kashim Shettima ne a gaba a wanda APC ta ke la'akari.

Majiyoyi dabam-dabam sun shaidawa jaridar cewa an yi zama da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a kan maganar tikiti, kuma ya nuna masu Sanatan ne zabinsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Bada Satar Amsa Kan Wanda Zai Zama Abokin Takarar Tinubu

Majiyar ta tabbatar da cewa jam’iyyar APC za tayi tikitin Musulmi da Musulmi ne a zaben 2023.

Ina batun Simon Lalong?

Da aka tambaya ko akwai yiwuwar Bola Tinubu ya dauko, Simon Lalong tun da kirista ne, sai majiyar ta nuna babu maganar tafiya da Gwamnan na Filato.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda wannan majiya ta bayyana, na-kusa da Tinubu su na ganin ya kamata ayi wa Sanata Shettima sakayya saboda irin kokarin da ya yi a tafiyar.

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ba a gama magana ba tukuna

“Babu abin da ya tabbata zuwa yanzu. Sunansa yana cikin wadanda aka ambata. Ba a kawo sunayen saura kamar yadda aka ambaci Shettima ba.”
“Ana kawo maganar irinsu Boss Mustapha, amma Shettima ne na farko da ake tunani.”

- Majiya

Yau za a san abokin takarar Tinubu

A wani rahoton, an tabbatar da cewa Bola Tinubu zai fadawa Duniya wanda za su yi takara da shi a APC mai mulki daga yanzu zuwa yammacin yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Ba Mu Yarda Da Musulmi 2 Ba: Kungiya Ta Bayyana Kirista Da Yafi Dace Wa Tinubu Ya Dauka a Matsayin Mataimaki a 2023

Daga cikin wasu sunayen da ake ambata akwai tsohon Sakataren kungiyar Buhari Support Group, Alhaji Kabir Ibrahim Masari da kuma Dr. Ibrahim Bello Dauda.

Tun zamanin ANPP Kabir Ibrahim Masari yake tare da Muhammadu Buhari. Shi ma Dr. Ibrahim Bello Dauda ya fito ne daga tsakin ‘yan CPC a jam’iyyar APC.

Ba na katsalandan - Buhari

An ji labari cewa Garba Shehu ya ce yadda zaben ‘dan takaran shugaban kasa ya kasance ba tare da rigima a APC ba, ya nuna shugaban kasa bai nuna son kai ba.

Garba Shehu ya wanke Mai gidansa daga zargin cusa bakinsa a sha'anin wanda zai gaje shi a 2023, ya ce babu mahalukin da yake juya Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel