Zaben fidda gwanin APC: Ba zan janye wa kowane dan takara ba, inji Yahaya Bello

Zaben fidda gwanin APC: Ba zan janye wa kowane dan takara ba, inji Yahaya Bello

  • Gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana cewa ba zai janye daga takara ba
  • Ya bayyana haka ne daidai lokacin da wasu 'yan takara ke ta janyewa saboda marawa Osinbajo baya
  • Ya bayyana cewa, yana da deliget masu yawa, kuma zai iya kawo kujerar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa

Gwamnan jihar Kogi, kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, ya sha alwashin ba zai sake ya janyewa wani dan takara a zaben fidda gwani na shugaban kasa ba, yana mai cewa yana da kyakkyawar dama ta lashe zaben, Vanguard ta ruwaito.

Bello na daga cikin mutane 10 da kwamitin Cif John Odigie-Oyegun ya tantance, har ta kai ga gwamnonin Arewa 13 suka yi shawarin mika tikitin takara zuwa Kudu tare da kara datse 'yan takara zuwa biyar ba tare da tuntubar 'yan takara ba.

Kara karanta wannan

Kebbi: Shugaban masu rinjaye a majalisa ya fice daga APC ya koma jam'iyyar PDP

Batun Yahaya Bello kan janyewa daga takara
Zaben fidda gwanin APC: Ba zan janye wa kowane dan takara ba, inji Yahaya Bello | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake magana da manema labarai a dandalin Eagle Square a gefen zaben fidda gwanin, ya ce ba zai janye ba saboda:

“Ina da kyakkyawar dama ta lashe zaben fidda gwanin. Na tabbata ina da sama da 50% cikin 100% na deliget.”

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bello a baya ya ce idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukace shi da ya janye daga takarar zai yi hakan.

Duk da haka, ya ce:

"Ba zan janye ba saboda yanzu na gana da Shugaban kasa kuma bai nemi in janye wa kowa ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel