Rikicin Siyasar Kano: Laifin Wanene? Mai Fashin Baki Ya Yi Cikakken Bayani

Rikicin Siyasar Kano: Laifin Wanene? Mai Fashin Baki Ya Yi Cikakken Bayani

  • An yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki matakai da za su taimaka wurin kashe wutar siyasar da ke ruruwa a jihar Kano
  • Masu zanga-zanga sun fita tituna a Kano bayan hukuncin Kotun Daukaka Kara ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • A rahotonsa, wani manazarci ya bayyanawa Legit.ng wasu abubuwan da rikicin siyasan za su iya haifarwa a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Al'ammuran siyasa sun dau zafi a jihar Kano tun bayan da Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da kwace kujerar Gwamna Abba Yusuf na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Kotun ta bai wa Nasiru Gawuna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) nasara.

Abba da Gawuna
Bangaren shari'a na daga cikin wadanda suka janyo rikicin siyasa a jihar Kano. Hoto: Nasiru Gawuna/Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Jigon LP ta bayyana wanda ya kamata Kotun Koli ta ayyana a matsayin gwamnan Kano

A ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba, mutane da ake ce magoya bayan Abba ne sun fito titunan Kano suna zanga-zanga kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Zanga-zangan ta yi zafi bayan wasu yan daba sun yi arangama da yan sanda.

Legit.ng ta rahoto cewa arangamar ta yi sanadin mutuwar mutum daya, wasu biyu kuma sun jikkata bayan yan sanda sun yi harbi don tarwatsa masu zanga-zangan.

Da ya ke martani kan siyasar Jihar Kano, mai fashin baki kan al'amuran yau da kullum Dr Abubakar Sani bayyana lamarin a matsayin abu mai sammatsi.

A hirarsa da Legit.ng, Dr Sani ya ce akwai laifin bangaren shari'a a rikicin da ke faruwa a jihar ta arewa maso yamma.

Ya ce:

"Ina ganin ya kamata bangaren shari'ar mu ya dauki wani bangare na laifin saboda gazawarsu da yadda suke yanke hukunci mai cike da kura-kurai da sabanni.
"Dole bangaren shari'a ya yi abin da ya dace sannan ya fanshe kimartsa da ya riga ya zube a idanun yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin sunayen manyan yan siyasa 4 da tsohon gwamnan Ribas ya raba gari da su

Tasirinsa ga tattalin arziki

Fitaccen masanin tattalin arziki na Nigerian Economic Summit Group (NESG), Paul Alaje ya fada wa Legit.ng cewa idan aka samu wani tashin hankali a Kano zai shafi tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce dole gwamnati ta tashi ta dauki matakin gaggawa saboda kare tattalin arziki kafin ya baci.

Da ya ke jadada ra'ayin Dr Sani, Alaje ya yi kira ga bangaren shari'a ta yi abin da ya dace saboda zaman lafiya.

Ya ce:

"Ina son kira ga ma'aikatan shari'a su yi abin da ya dace domin zaman lafiya. Kamar yadda ake cewa, ba'a samun zaman lafiya sai da adalci.
"Idan mutane suka cigaba da zanga-zanga a yanayi da ka iya tabarbarewa irin na Kano, ina fargabar zai kama da wuta. Idan ya kama da wuta, dole mu yi taka-tsantsan kada ya shafi rayyuka da dukiyoyi. Wannan shine dalilin da yasa dole gwamnati ta yi a hankali da Kano."

Asali: Legit.ng

Online view pixel