Zaben 2023: Jerin ministocin Buhari da suka ki ajiye aiki bayan ayyana tsayawa takara

Zaben 2023: Jerin ministocin Buhari da suka ki ajiye aiki bayan ayyana tsayawa takara

Duk da umurnin da shugabancin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya baiwa masu rike da mukaman siyasa da ke neman takarar kujeru na su yi murabus wata guda kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, wasu ministocin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke hararar kujerun shugabanci a 2023 basu aikata hakan ba har yanzu.

Rashin ajiye aikin nasu ya kuma sabama sashi na 84(12) na dokar zabe, wacce ta nemi a ajiye aiki kafin shiga zaben fidda gwani.

Zaben 2023: Jerin ministocin Buhari da suka ki ajiye aiki bayan ayyana tsayawa takara
Zaben 2023: Jerin ministocin Buhari da suka ki ajiye aiki bayan ayyana tsayawa takara Hoto: APC
Asali: Twitter

Ga jerin sunayen ministocin da suka bijirewa jam’iyyar

1. Rotimi Amaechi (Sufuri)

Rotimi Chibuike Amaechi, ministan sufuri ya kasance dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Tsohon gwamnan na jihar Ribas kuma babban jigon jam’iyyar mai mulki na daya daga cikin yan tsirarun ministocin da suka ki yin murabus duk da umurnin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Chris Ngige, (Kwadago da samar da ayyukan yi)

Ngige, ministan kwadago da samar da ayyukan yi da yake bijirewa umurnin jam’iyyarsa, ya ce ba zai yi murabus daga kujerarsa ba.

Ya ce bai da masaniya a kan wata doka da ta nemi ya ajiye aiki kafin ya shiga tseren neman tikitin shugaban kasa na APC akalla kwanaki 30 kafin gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Da aka tunatar da shi cewa APC ta bukaci dukka ministoci su yi murabus, sai ya ce:

“A’a, baya ciki, baya cikin aikin kwata-kwata. Amma zan yi wasu tuntuba da jam’iyyar, zan binciko da kaina.
“Ban ga wannan sanarwar daga jam’iyyar ba. Ban ga wani sako daga jam’iyyar ba. Ba a isar da shi gare ni ko ga wani ba. Ni mai neman takara ne, ni dan takarar shugaban kasa ne. Don haka zan gano kuma idan gaskiya ne, to zan san abin da zan yi.”

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

3. Chukwuemeka Nwajiuba (Karamin ministan ilimi)

Karamin ministan ilimi, Hon. Emeka Nwajiuba wanda ya ayyana kudirinsa na takarar zaben shugaban kasa a 2023 ya soke batun yiwuwar ajiye mukaminsa gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC.

“Murabus din minista ko duk wanda ke kan mukami yana karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya ne.
“An bukaci da muyi takarar zabe idan muna so. An bukaci da mu yi murabus kwanaki 30 kafin kowani zabe da muke neman takara. Wannan shine matsayin doka. Duk wani mutum na iya kasancewa da ra’ayi."

4. Abubakar Malami, Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari’a

Ministan shari’a kuma Atoni Janar na tarayya, Abubakar Malami, ya ce yana sha’awar yin takarar kujerar gwamnan Kebbi. Wata daya kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar, babban ministan ya ki bin umurnin jam’iyyar ta hanyar gabatar da takardarsa ta ajiye aiki.

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

Kara karanta wannan

Sanatan Kebbi ta tsakiya: Alaka ta yi tsami tsakanin Aliero da Gwamna Bagudu kan wanda zai mallaki tikitin APC

A wani labarin, ministan sufuri kuma, Rotimi Amaechi ya jadadda biyayyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin da yake shirin neman shugabancin kasar a 2023.

Wata sanarwa daga ofishin labaransa ya ce Amaechi ya magantu ne a lokacin wata ganawa da shugabanni, wakilai da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar APC ta jihar Ribas a ranar Juma’a, Daily Trust ta rahoto.

Ya bayyana cewa a yunkurinsa na son zama shugaban kasar Najeriya wanda ya cancanci hawa kujerar, bai kasance mai gaggawa ko rashin biyayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng