Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

  • Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa koda Buhari bai zabe shi ba a matsayin shugaban kasa, zai ci gaba da yiwa APC biyayya
  • Amaechi ya ce shi mutum ne mai tsanananin biyayya kuma a shirye yake ya marawa duk wanda shugaban kasar ya zaba baya
  • Dan takarar shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wakilan APC a Ribas a ranar Laraba, 29 ga watan Afrilu

Ministan sufuri kuma, Rotimi Amaechi ya jadadda biyayyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yayin da yake shirin neman shugabancin kasar a 2023.

Wata sanarwa daga ofishin labaransa ya ce Amaechi ya magantu ne a lokacin wata ganawa da shugabanni, wakilai da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a sakatariyar APC ta jihar Ribas a ranar Juma’a, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba
Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa a yunkurinsa na son zama shugaban kasar Najeriya wanda ya cancanci hawa kujerar, bai kasance mai gaggawa ko rashin biyayya ba.

Amaechi ya yi bayanin cewa abun bakin ciki ne cewa yan siyasa da dama basu fahimci manufar biyayya ba.

Ya yi ikirarin cewa idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar zabar wani daban a matsayin dan takarar shugaban kasa a maimakon shi, zai marawa mutumin baya, rahoton The Cable.

“Biyayya ba shine idan ba a zabe ka ba, sai ka bijire; biyayya na nufin ka bi mutumin da ke jagorantarka. Ni mutum ne mai biyayya sosai kuma wadanda basa biyayya, ina musu fatan alkhairi; wadanda ke son yin duk abun da suke son yi, ina masu fatan alkhairi.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

“Za a ba kowa dama; za mu yi takarar wannan zabe na shugaban kasa; za mu yi takara, kuma ina biyayya ga shugaban kasa kuma ina biyayya ga jam’iyya, duk abun da jam’iyya ta zaba, zan mara masa baya. Idan jam’iyya da shugaban kasa suka koma wanene, zan marawa mutumin baya; idan jam’iyya ta zabe ni, zan ji dadi sannan nagode ma Allah.”

Sanatan APC Okorocha ya karbi fom din takarar shugaban kasa a zaben 2023

A gefe guda, mun ji a baya cewa kungiyar TNN ta samarwa da sanata Rochas Okorocha fom din nuna sha'awa da tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC.

Hakan na zuwa ne daidai lokacin da jiga-jigan jam'iyyar APC ke ci gaba da biyan makuda milliyoyi domin nuna sha'awarsu da gaje kujerar shugaba Buhari.

A wata sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Facebook, Okorocha ya bayyana cewa, a yau karbi fom din ne a yau Juma'a 29 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel