2023: Saraki, Tambuwal Da Wasu 'Yan Takara 2 a PDP Sun Amince Da Fitar Da Ɗan Takara Ta Hanyar Sasanci

2023: Saraki, Tambuwal Da Wasu 'Yan Takara 2 a PDP Sun Amince Da Fitar Da Ɗan Takara Ta Hanyar Sasanci

  • Yan takarar shugaban kasa na PDP a kalla guda hudu sun amince da amfani da hanyar sasanci don tsayar da dan takara
  • Yan takarar sun sanar da hakan ne bayan da suka kai wa Gwamna Okezie Ikpeazu na Jihar Abia ziyara a ranar Talata
  • Bukola Saraki, da ya yi magana a madadin yan takarar ya ce sun cimma wannan matsaya ne don ceto Najeriya ya fi burin kowannen cikinsu

Abia - A kalla yan takarar shugaban kasa hudu a karkashin jamyyar PDP ne suka ce za su da sasanci domin ganin jam'iyyar ta yi nasara a babban zaben shekarar 2023, rahoton Premium Times.

Yan takarar sun sanar da hakan ne yayin yi wa manema labarai jawabi bayan ziyarar da suka kai wa Gwamna Okezie Ikpeazu na Jihar Abia a gidansa da ke garinsu Umuobiakwa a karamar hukumar Obingwa a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

2023: Saraki, Tambuwal Da Wasu 'Yan Takara 2 a PDP Sun Amince Da Fitar Da Dan Takara Ta Hanyar Sasanci
2023: Saraki, Tambuwal Da Wasu 'Yan Takara a PDP Sun Amince Da Fitar Da Dan Takara Ta Hanyar Sasanci. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Dalilin da yasa 'yan takarar na PDP suka amince da sasanci?

Da ya ke magana a madadin sauran yan takarar, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya ce sun cimma wannan matsayar ne saboda kishi da cigaban Najeriya.

Ya ce rayuwa da walwalar yan Najeriya ya fi duk wani buri na dan takara.

Ya ce:

"Yan Najeriya na cikin wahala da rashin tsaro.
"Wadannan abubuwan da suke faruwa a kasar da suka sa wasu daga cikinsu suka tabbatar suna yin abin da ya dace ne.
"Ina son in tabbatar wa yan Najeriya cewa abin da muka sa gaba shine ganin kasar nan ta gyaru.
"Idan wannan shine sadaukarwar da za mu yi don sauya abubuwa a Najeriya, muna son sanar da yan Najeriya cewa a shirye muke mu aikata hakan."

Kara karanta wannan

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

Yanzu Jihar Enugu ta rage mana mu tafi mu ga gwamna don neman goyon bayansa, Saraki

Vanguard ta rahoto Saraki ya ce sun tafi Enugu ne domin neman goyon bayan gwamnan wurin ganin sasancin ya yi nasara, yana mai cewa wannan shine karo na farko da yan takarar suka hadu da kansu don yin sasanci.

Ya ce duk da cewa abu ne mai wahala, sun yi imanin cewa shine alheri ga Najeriya.

Ya kara da cewa za su tafi Enugu domin ganin gwamnan jihar daga nan kuma sun kammala ziyarar gwamnonin PDP 19 don neman goyon bayansu.

NAN ta rahoto cewa yan takarar sun hada da Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Mohammed Hayatudeen.

Ba A Ga Atiku Ba A Taron Da Wike Ya Yi Da Masu Neman Takarar Shugaban Ƙasa Na Jam'iyyar PDP

A wani labarin, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya bai halarci taron sirrn da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya shirya ba tare da wasu ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ba, yayin da zaben fidda gwanin jam’iyyar ya ke karatowa.

Kara karanta wannan

Borno: Dubun ƴan ta'adda ta cika, soji sun ragargajesu tare da ceto mata da ƙananan yara

An tattaro yadda ‘yan takarar suka dade suna tattaunawa dangane da wanda zai tsaya takara don gudun tashin tarzoma ta cikin jam’iyyar yayin zaben, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar da suka halarci taron da aka yi gidan gwamnati da ke Port Harcourt sun hada da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed; Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal; tsohon manajan darekta na bankin kasa da kasa na FSB, Dr. Mohammed Hayatu-Deen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164