An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

  • Wasu tsagerun yan bingida sun kai munanan hare-hare a kauyuka hudu da ke karamar hukumar Kunam ta jihar Filato a ranar Lahadi
  • Harin da aka kai garuruwan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram, ya yi sanadiyar mutuwar mutane masu yawan gaske tare da asarar dukiyoyi
  • Dan majalisa mai wakiltan mazabar Kanam a majalisar dokokin jihar, Saleh Yipmong, ya tabbatar da kai hare-haren

Plateau - Yan bindiga sun farmaki kauyuka hudu a yankin karamar hukumar Kunam da ke jihar Filato a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu, jaridar Premium Times ta rahoto.

An tattaro cewa harin wanda ya wakana a garuruwan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.

Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa an tabbatar da mutuwar fiye da mutum 70 a harin na ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sabon hari: An kashe sabon sarkin gargajiya a yankin Kaduna, da wasu mutum 14

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4
An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4 Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Harin ya kuma gudana ne a ranar da rundunar yan sandan jihar Filato ta yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa yan bindiga sun shigo garin Jos kuma suna iya kai farmaki a kowani lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Jos, ya ce rundunar ta dauki wani sabon salo na dakile matsalar rashin tsaro a jihar.

Wani mazaunin garin Kukawa, Adam Musa, ya fadama Daily Trust cewa mutane da dama sun jikkata yayin da daruruwan mutane suka gudu suka bar gidajensu bayan hare-haren.

Musa ya ce yan bindigar a hare-hare mabanbanta sun farmaki kauyukan da misalin karfe 11:00 na safe sannan suka cinnawa gidaje da yawa wuta.

Ya kara da cewa:

“Wadanda suka rasa rayukansu suna da yawa. A zahirin gaskiya sun kai kimanin 15 ko 20 da aka kashe. Wadanda aka kashe suna da yawa. Ba zan iya bayar da adadin ba a yanzu saboda har yanzu muna kwasan gawarwaki.”

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun kai mummunan hari Sakatariyar karamar hukumar da gwamna ya fito

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, kakakin yan sandan jihar ya yi alkawarin sake kira amma bai aikata hakan ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Amma wani dan majalisa mai wakiltan mazabar Kanam a majalisar jihar, Saleh Yipmong, ya tabbatar da harin.

Ya ce:

“An sanar da ni cewa an rasa rayuka da dukiya. A yanzu haka, gwamnati ta tura jami’an tsaro yankin.
“Ina kira ga mutanen yankin da su ba hukumomin tsaro hadin kai don tabbatar da dawowar zaman lafiya a yankunan da abun ya shafa.”

Hakazalika, mamba mai wakiltan mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar tarayya, Yusuf Adamu Gagdi, ya tabbatar da harin.

Dan majalisar, wanda ke jagorantar kwamitin majalisa kan sojojin ruwa, ya koka cewa hare-haren ya wakana a wurin duk da rahoton sirri da DSS ta bayar game da tserewar yan bindiga zuwa Filato da jihohin da ke makwabtaka kimanin watanni tara da suka gabata.

Kara karanta wannan

Ya isa haka: Al'ummar Plateau sun fito nuna alhininsu ga barnar 'yan bindiga

Ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta yi sakaci wajen samar da tsaro ga al’ummar Filato.

Batun rashin tsaro: Tsohon ministan Buhari ya yiwa shugaban kasar wankin babban bargo

A gefe guda, tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gazawa yan Najeriya sannan cewa ya baiwa mutane da dama kunya ciki harda shi saboda ya kasa magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Dalung ya bayyana hakan ne a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, 10 ga watan Maris.

Tsohon ministan ya kuma koka kan cewa shugaban kasar na raba iko tare da kasurgumin shugaban yan bindiga na arewa maso yamma, Bello Turji da kuma mayakan ISWAP sakamakon gazawarsa wajen magance rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel