2023: Babban 'Dan adawa, Kwankwaso ya na daf da kammala shirye-shiryen barin PDP, ya koma APC

2023: Babban 'Dan adawa, Kwankwaso ya na daf da kammala shirye-shiryen barin PDP, ya koma APC

Jita-jita na yawo cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai bar jam’iyyar adawa

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai jin dadin irin zaman da ake yi a PDP

Idan ta tabbata, tsohon Ministan zai iya komawa APCn da ya baro a 2018

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya kusa karkare shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar hamayya ta PDP, inda ake tunani zai koma APC.

Politics Digest ta fitar da rahoto cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso bai jin dadin zamansa a PDP, don haka ya ke harin ya koma APC mai mulki da ya baro.

Rabiu Kwankwaso wanda ya wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019 ya tattauna da shugaban riko na APC, gwamna Mai Mala Buni.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP za ta sasanta Sanata Kwankwaso da Tambuwal

Daga cikin wadanda su ke kokarin dawo da Rabiu Kwankwaso tafiyar APC akwai gwamna Badaru Abubakar da Muhammad Bello Matawalle wanda ya bar PDP.

Sauya-sheka za ta raba kan 'Yan Kwankwasiyya da APC

Idan hakan ta tabbata, ana tunani Kwankwaso zai bar PDP tare da wasu manyan yaransa irinsu Injiniya Abba Kabir Yusuf da Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo.

Amma wasu daga cikin ‘Yan Kwankwasiyya ba za su sauya-sheka zuwa jam’iyyar ta APC ba.

Kwamishinan raya karkara na Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya ce su na murna da wannan lamari, amma ya gargadi tsohon gwamnan a kan kawo rikici a APC.

Rabiu Musa Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasiyyareportersNegeria
Asali: Facebook

KU KARANTA: Buba Galadima ya fara nuna akwai matsala a tafiyar PDP

“Idan har ya zo, ya sani akwai shugaba a jam’iyyar, kuma shi ne Dr. Abdullahi Umar Ganduje, dole ya bi shi kamar yadda ya yi masa biyayya da yake kan mulki.”

Abin da ya fara jawo matsala

Tun bayan da rikici ya barke wajen zaben shugabannin jam’iyyar PDP da aka yi garin Kaduna a Afrilu, Rabiu Musa Kwankwaso ya fara ya tunanin sauya-sheka.

Jaridar ta ce tun wancan lokaci magoya bayan tafiyar ‘dan siyasar su ka fahimci cewa ba za su samu kujerar mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa ba.

Yayin da tsohon Ministan tsaron yake goyon bayan Mohammed Jamo Yusuf, ana zargin cewa gwamnan jihar Sokoto ya na mara wa Bello Hayatu Gwarzo baya.

Rahoton ya ce bayan abin da ya faru ne Sanata Kwankwaso ya fara gana wa da wasu manyan APC irinsu Bola Ahmed Tinubu, wanda su ka zauna a Saudi Arabia.

Asali: Legit.ng

Online view pixel