Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe

  • Hawaye sun kwaranya yayin da aka yi jana'izar mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da yan bindiga suka kai garuruwan Filato
  • An tattaro cewa an binne kimanin sama da mutane 100 wadanda harin ya ritsa da su a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu
  • Rundunar yan sandan jihar ta bayyana cewa an tura jami'an tsaro zuwa yankin da abun ya faru amma bata bayyana adadin wadanda aka kashe ba

Plateau - Rahotanni sun kawo cewa an yi jana’izar mutanen da yan bindiga suka kashe a harin safiyar Lahadi da suka kai kauyuka hudu na jihar Filato.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa masoya da abokan arziki ne suka binne mamatan gaba daya a ranar Litinin, 11 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da motoci biyu na matafiya a jihar Ribas

Mazauna yankunan sun bayyana cewa an samo sama da gawarwaki 100 kuma an binne su amma kuma babu wani adadi da rundunar yan sanda ko gwamnatin jihar ta fitar a hukumance.

A baya Legit Hausa ta rahoto yadda yan bindiga suka farmaki kauyuka hudu a yankin karamar hukumar Kunam da ke jihar Filato a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu. Harin ya wakana a garuruwan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram.

Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe
Kisan gilla a Plateau: Tashin hankali yayin da aka yi jana'izar mutane sama da 100 da 'yan bindiga suka kashe Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daily Trust ta kuma rahoto cewa an samo gawarwakin wasu da suka yi kokarin tsere ma harin daga wasu jeji da ke kusa a ranar Litinin.

Kakakin yan sandan jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya ce an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin amma bai ce komai ba game da adadin wadanda suka mutu.

Kara karanta wannan

Ashe makiyaya ne ba ‘Yan bindiga ba – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan bidiyon da ke yawo

Gabriel ya ce:

“Ban samu karin bayani game da adadin wadanda aka kashe da gidajen da aka kona ba tukana, zan sanar da kafar watsa labarai da zaran na samu."

Sai dai kuma, Alhaji Dayyabu Garga, shugaban karamar hukumar Dangi wanda a karkashinsa ne kauyukan suke, ya tabbatar da cewa an binne sama da mutane 100.

“Ni da sauran mutane mun ziyarci kauyukan da abun ya shafa. Mun binne sama da mutum 100 tare da mutanen yankin. Amma an tura jami’an tsaro don dawo da oda. Wannan shine karo na farko da muke fuskantar wannan ibtila’I a Kanam.”

Adam Musa, wani mazaunin Kukawa ya sanar da Daily Trust cewa an kashe mutane 45 a Kukawa, 31 a Gyanbahu, shida a Dungur sannan 31 a Keram.

Ya kara da cewa an tura mutane da yawa asibitoci daban-daban ciki harda babban asibitin Dangi da ke karamar hukumar Kanam domin jinya.

Kara karanta wannan

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

A halin da ake ciki Gwamna Simon Bako Lalong ya umarci jami’an tsaro a jihar da su bi sahun wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Gwamnan a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na jihar, Dakta Makut Simon ya fitar, ya sha alwashin wahalar da yan ta’adda da sauran miyagu da suka kafa sansani a yankunan jihar.

Ya kuma umurci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jiha da hukumar samar da zaman lafiya da su gaggauta kai ziyara yankunan, su tantance halin da ake ciki tare da bayar da agaji tare da kula da wadanda suka jikkata.

An kashe mutane masu yawan gaske yayin da yan bindiga suka farmaki kauyukan Filato 4

Mun dai ji cewa yan bindiga sun farmaki kauyuka hudu a yankin karamar hukumar Kunam da ke jihar Filato a safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Afrilu, jaridar Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan bindiga sun kai mummunan hari Sakatariyar karamar hukumar da gwamna ya fito

An tattaro cewa harin wanda ya wakana a garuruwan Kukawa, Gyanbahu, Dungur da Keram, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa.

Jaridar Vanguard ta kuma rahoto cewa an tabbatar da mutuwar fiye da mutum 70 a harin na ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel