Atiku, Ribadu, Tambuwal, da wadanda suka yafe neman Shugaban kasa, su ka nemi Gwamna

Atiku, Ribadu, Tambuwal, da wadanda suka yafe neman Shugaban kasa, su ka nemi Gwamna

  • An yi wasu ‘yan siyasa da suka dauko ta da zafi a siyasar Najeriya, daga baya suka bari ya huce
  • Akwai wadanda a tashin farko suka nemi kujerar shugaban kasa, sai su ka koma takarar gwamna
  • Zama shugaba a kasa irin Najeriya yana da matukar wahalar gaske, abin sai wanda yake da rabo

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta bi tarihi, ta kawo sunayen irin wadannan ‘yan siyasa da suka fara da babban buri, amma dole suka hakura daga bisani:

1. Atiku Abubakar

Na farko a wannan jerin shi ne Alhaji Atiku Abubakar wanda ya nemi takarar shugaban kasa a zaben 1993, amma ya rasa tikitin SDP a wajen Marigayi MKO Abiola.

Daga baya Atiku ya hakura da shugaban kasa, ya yi takarar gwamna, kuma ya yi nasara a 1999. Duk da ya ci zabe, bai yi gwamna ba, ya zama mataimakin shugaban kasa

Kara karanta wannan

Lissafi ya canza: Shugaban kasa ya bada sabon umarni a kan zaben shugabannin jam’iyya

2. Nuhu Ribadu

Shi kuma Mallam Nuhu Ribadu ya shiga siyasa ne da neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar AC. Sai dai tsohon shugaban na EFCC bai yi nasara a 2011 ba.

Bayan kusan shekaru uku sai Ribadu ya nemi kujerar gwamnan jihar Adamawa a PDP. A nan ma dai bai dace ba, daga baya ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Atiku da Tambuwal
Aminu Waziri Tambuwal da Atiku Abubakar Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

3. Aminu Waziri Tambuwal

Da farko Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya nemi ya yi takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2015, a lokacin shi ne shugaban majalisar wakilan tarayya na kasa.

Idan za a tuna, Aminu Tambuwal ya hakura da wannan buri a APC, ya zama gwamna a jihar Sokoto. Kusan wannan abin ya maimaita kansa a PDP a zaben 2019.

Kara karanta wannan

Yadda mutane kusan 200 za su goge raini wajen neman mukamai 22 a Jam’iyyar APC

4. Datti Baba Ahmed

Dr. Datti Baba Ahmed yana cikin wadanda suka nemi tikitin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP a 2018, amma sam bai kama hanyar nasara ba.

Da aka dawo 2022 sai aka ji ‘dan siyasar ya na so ya yi takarar gwamna a jihar Kaduna. Dr. Baba Ahmed zai gwabza da APC mai mulki idan PDP ta ba shi tuta.

5. Rochas Okorocha

Sanata Rochas Okorocha ya taba neman ANPP ta tsaida shi a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a 2003, amma bai yi nasara ba. Daga nan sai aka ji ya koma PDP.

Okorocha ya kafa jam’iyyar AA da niyyar zama ‘dan takarar shugaban kasa a 2007, shi ma hakan bai yiwu ba. A karshe dai ya lashe zaben gwamnan Imo a zaben 2011.

Matsayin Yarbawa a 2023

A jiya aka ji cewa ba dole ba ne mulki ya fada hannun su Asiwaju Bola Tinubu ko Yemi Osinbajo domin ba a tsaida wata yarjejeniya da Yarbawa a jam’iyyar APC ba

Kara karanta wannan

Kan gwamnoni da jiga-jigai ya yi kwari, sun shirya yakar ‘Yan takarar Buhari a zaben APC

Akwai masu ganin kafin a kafa APC shekaru goma da suka wuce, sai da aka yi yarjejeniyar bayan Muhammadu Buhari, shugabanci zai koma kasar Yarbawa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel