Da dumi-dumi: Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban APC na kasa, ya bayyana dalili

Da dumi-dumi: Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban APC na kasa, ya bayyana dalili

  • Sanata Ali Modu Sheriff ya hakura ya janye daga tseren kujerar shugaban jam'iyyar APC na kasa yayin da babban taronta ke kara karatowa
  • Tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce ya janye ne saboda tsarin yanki na jam'iyyar wacce ta mika kujerar ga arewa ta tsakiya
  • Sai dai ya ce zai sake shiga tsere idan har jam'iyyar ta sauya ra'ayinta daga nan zuwa ranar Juma'a

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, jaridar Vanguard ta rahoto.

Hakan na zuwa ne yan kwanaki kafin babban taron jam’iyyar mai mulki na kasa wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Da dumi-dumi: Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban APC na kasa
Ali Modu Sheriff ya janye daga takarar kujerar shugaban APC na kasa Hoto: dailypost.ng
Asali: Facebook

Dalilinsa na janyewa daga tseren kujerar

A wata yar takaitacciyar hira a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris, a Abuja, Sheriff ya ce ya janye ne saboda tsarin rabon mukamai na jam’iyyar wacce ta mika kujerar zuwa ga yankin arewa ta tsakiya.

Sheriff wanda ya fito daga yankin arewa maso gabas ya bayyana cewa zai sake shiga tseren idan jam’iyyar ta canja shawararta tsakanin yanzu zuwa Juma’a, Daily Trust ta rahoto.

Buhari bai lamunce mun don darewa kujerar shugaban APC na kasa ba – Sanata Abdullahi Adamu

A gefe guda, mun ji cewa tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma babban dan takarar kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana cewa sabanin abun da ke ta yawo a kafafen yada labarai, Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai tsayar da shi ba.

Sanata Adamu ya yi karin hasken ne a Keffi yayin da ya karbi bakuncin jami’an jam’iyyar a matakin karamar hukuma a mahaifarsa ta Keffi, a ranar Asabar, Nigerian Tribune ta rahoto.

Idan za ku tuna, a yayin ganawar karshe da APC ta yi, an tattaro cewa shugaban kasar ya tsayar da Sanata Adamu kuma cewa hakan bai yiwa masu ruwa da tsaki da gwamnonin jam’iyyar dadi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel