Yadda Mai Mala Buni ya yi yunkurin hana zaben shugabannin APC na kasa

Yadda Mai Mala Buni ya yi yunkurin hana zaben shugabannin APC na kasa

  • Mai Mala Buni ya dauki matakan zagon kasa ga zaben shugabannin jam'iyyar APC na kasa, wanda za'a gabatar a 26 ga watan Maris
  • An gano yadda shi da sakataren kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar suka yi kokarin samun umarnin kotu na wucin-gadi don hana jam'iyyar gabatar da taron
  • A halin yanzu, gwamnonin jam'iyyar APC dake goyon bayan sa a da, sun koma bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari

Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe, korarren shugaban kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC, ya dauka matakan zagon kasa ga zaben jam'iyyar na kasa, wanda za'a gabatar a ranar 26 ga watan Maris, The Cable ce ta ruwaito hakan.

A lokacin da ake tsaka da rikicin cikin gida a jam'iyya mai mulkin a kan gangamin taron zaben shugabannin jam'iyyar, Buni ya tsaya a kan bakan sa na takarar shugaban jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Tuna baya a APC: Abubuwan da suka faru har gwamnan Neja ya maye gurbin Buni

Yadda Mai Mala Buni ya yi yunkurin hana zaben shugabannin APC na kasa
Yadda Mai Mala Buni ya yi yunkurin hana zaben shugabannin APC na kasa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

The Cable ta ruwaito yadda ya zabi ya tsaya a ofishin da ke dab da rusa shirin gangamin taron zaben shugabannin jam'iyyar.

Gwamnan jihar Yobe ya dade yana jan kafa a kan shirye-shirye da lamurran da suka shafi zaben shugabannin jam'iyyar.

Sai dai, ba tare da sanin mambobin jam'iyyar ba, Buni da John Akoanudoedehe, sakataren kwamitin rikon kwaryar jam'iyyar APC na kasa, sun kyankyashe tuggun da suka hada don juya akalar jam'iyyar.

The Cable ta gano yadda suka yi amfani da wani don samun umarnin kotu na wucin-gadi na hana jam'iyyar mai mulki gabatar da zaben shugabannin jam'iyyar, har sai an saurari karar an yanke hukunci.

Salisu Umaru ya shigar da karar APC da Buni a babbar kotun tarayya (FCT)

"Cewa mai kare kansa na farko ko wanda ake karar, zai iya shirya zaben shugabannin jam'iyya na kasa bayan sauraro da fuskantar hukuncin gaban wannan kotun mai daraja bisa abunda ake kararsa a kai," umarnin kotun da The Cable ta karanta.

Kara karanta wannan

Sabon rikicin APC: Buhari ya sanya mun albarka – Gwamnan Neja

The Cable ta fahimci yadda hakuncin Buhari kan Buni ya janyo wa gwamnan jihar Yobe zamewar takwarorin shi, wadanda a da suke goyon bayan sa.

An gano yadda Muhammad Badaru, gwamnan jihar Jigawa; Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna; Atiku Bagudu, gwamnan jihar Kebbi; da Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi suka juya wa Buni baya, a cewar wata majiyar.

"A halin yanzu, Buni bai da mai tsaya mishi. Gwamnonin APC da suke goyon bayansa a da, suka koma goyon bayan Shugaban kasa," majiyar ta kara bayyana hakan.

Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar APC ta kasa dake Abuja

A wani labari na daban, jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja.

Akwai rahotannin da ke bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tunbuke gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, daga mukamin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar.

An tattaro cewa, gwamnan jihar Niger, Sani Bello ne zai karba ragamar jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar APC ta kasa dake Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel