2023: Tinubu Ya Lissafa Shahararrun 'Yan Siyasa Da Ya Taimakawa Suka Zama Gwamnoni

2023: Tinubu Ya Lissafa Shahararrun 'Yan Siyasa Da Ya Taimakawa Suka Zama Gwamnoni

  • Gabanin zaben shugaban kasa na 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci sarakunan gargajiya a jihar Ondo don neman goyon bayansu
  • Da ya ke jawabi a fadar Deji na Akure, mai neman takarar shugaban kasar a jam'iyyar APC ya ce ya taimakawa mutane da dama cimma burinsu na siyasa
  • Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ambaci tsohon gwamnan Osun Aregbesola da wasu gwamnoni biyu cikin wadanda ya taimaka wa

Akure, Jihar Ondo - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jagora na kasa na jam'iyyar APC, ya ce ya taimakawa mutane da dama a kasar nan sun cimma burinsu na siyasa.

Tinubu, wanda ke neman takarar shugaban kasa a 2023 ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a 4 ga watan Maris, lokacin da ya ziyarci Deji na Akure a jihar Ondo, The Punch ta rahoto.

2023: Tinubu Ya Lissafa Shahararrun 'Yan Siyasa Da Ya Taimakawa Suka Zama Gwamnoni
2023: Tinubu Ya Lissafa Fitattun 'Yan Siyasa Da Ya Taimakawa Suka Zama Gwamnoni. @Official_ABAT
Asali: Twitter

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon gwamnan na Jihar Legas ya ziyarci masu sarautan gargajiya ne a yankuna uku a jihar Ondo, don neman goyon bayansu bisa takararsa.

Na taimaki Aregbesola, Mimiko da Fayemi - Tinubu

A jawabin da ya yi a fadar Deji na Akure, Tinubu ya ce ya taimaki Ogbeni Rauf Aregbesola da Dr Olusegun Mimiko samun nasara a kotu a jihohin Osun da Ondo.

Ya kuma ambaci gwamnan Jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi da Shugaba Muhammadu Buhari da wasu saura.

Kalamansa:

"Na taimaka wa Mimiko kwato hakkinsa a kotu bayan shekaru biyu da zabensa. Na taimaki Fayemi kwato hakkinsa bayan shekaru uku.
"Shekaru uku da watanni 10 aka kwashe kafin kwato hakkin Aregbesola. Mun taimaki wasu mutanen irin su."

2023: Sarkin Katsina Ya Goyi Bayan Tinubu Ya Gaji Kujerar Buhari

A wani rahoton, Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, ya nuna goyon bayansa ga takarar Sanata Ahmed Bola Tinubu na shugabancin kasa.

Ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tarbar wata tawagar kungiyoyin Arewa masu goyon bayan takarar shugabancin kasar Tinubu da suka kai masa ziyara a fadarsa a ranar Juma'a a Katsina.

Sarkin ya ce Tinubu ya cancanta kuma zai shayar da ƴan Najeriya romon demokradiyya, rahoton Nigerian Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel