Gagarumin abun al'ajabi ne da mu'ujiza tsira a karkashin mulkin Buhari, PDP

Gagarumin abun al'ajabi ne da mu'ujiza tsira a karkashin mulkin Buhari, PDP

  • Jam'iyyar PDP ta ce babbar mu'ujiza da abun al'ajabi ne tsira a kasar nan karkashin mulki gurbatacce irin na jam'iyyar APC
  • Babban jam'iyyar adawar ta ce 'yan Najeriya sun fuskanci rashin adalci, tabarbarewa tattalin arziki, kashe-kashe da rashin tsaro
  • Ta yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi tsaye tare da hada kai wurin farfado da kasar nan tare da kwato ta daga hannun gurbataccen shugabanci

Gagarumar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta taya 'yan Najeriya murnar zuwan sabuwar shekarar 2022.

A sakon murnar sabuwar shekarar da jam'iyyar PDP ta fitar ta hannun sakataren yada labaranta na kasa, Honarabul Debo Ologunagba, ta yi kira ga 'yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokacin wurin farfado da soyayya, haduwar kai, adalci tare da bukatar samun shugabanci nagari a kasar nan.

Gagarumin abun al'ajabi ne tsira a karkashin mulkin Buhari, PDP
Gagarumin abun al'ajabi ne tsira a karkashin mulkin Buhari, PDP. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jam'iyyar ta ce tsira a shekarar 2021 karkashin mulkin All Progressives Congress (APC) ba tuna baya kadai ya dace a yi ba, ya dace a hada da kokarin ganin cewa an ceto kasar nan daga mulkin kama karya.

Ya ce abun al'ajabi ne yadda kasar nan ta kwashe shekaru shida cikin "take hakkin dan Adam, kashe-kashe ba tare da yanke hukunci ba, rashin ababen more rayuwa, tsanani a fannin tattalin arziki, hauhawar ta'addanci da kuma kashe mutane wanda duk aka samu sanadiyyar mulkin APC."

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce sabuwar shekarar nan ta gabatar wa da kasar nan sabbin damammaki da za su yakice dukkan yaudara, tsoro da rashin tunani gefe tare da fuskantar dukkan kalubalen shugabanci gurbatacce kuma a yi aiki cike da hadin kai domin ceto kasar nan tare da gina ta.

Gwamnan Bayelsa ya rantsar da matarsa matsayin alkalin babbar kotu

A wani labari na daban, Gwamna Duoye Diri na jihar Bayelsa ya rantsar da matarsa, Patience Zuofa-Diri, da wasu masana shari'ar uku a matsayin alkalan babbar kotun jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Baya ga matar Diri, sauran sabbin alkalan sun hada da tsohon magatakardan babbar kotun jihar Bayelsa, James Lookie, lakcara a fannin shari'a na jami'ar Niger Delta, Dr. Simon Amaduobogha da kuma lauya Christine Enegesi.

A yayin basu rantsuwar kama aiki a matsayinsu na sabbin alkalai a gidan gwamnatin jihar da ke Yenagoa, Diri ya ce mulkinsa ya na bai wa fannin shari'a fifiko ganin irin rawar da suke takawa a al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel