Hadimin Ganduje da dubban magoya bayansa sun koma bangaren Shekarau

Hadimin Ganduje da dubban magoya bayansa sun koma bangaren Shekarau

  • Mai ba Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shawara kan harkokin jiha, Mohammed Shehu ya koma bangaren Sanata Ibrahim Shekarau na jam'iyyar All Progressives Congress
  • Shehu ya ce shi da dubban magoya bayansa sun koma sansanin Shekarau ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci na bangaren da Abdullahi Abbas ke jagoranta
  • Ya kuma ce magoya bayansa sun yanke shawarar yin kamfen domin nasarar Sanata Barau Jibrin a kudirinsa na takarar gwamna

Kano - Mohammed Shehu, hadimin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin jiha ya koma bangaren Sanata Ibrahim Shekarau na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a Kano.

Da yake jawabi ga dubban magoya bayan jam'iyyar a karshen mako a Kano, Mista Shehu ya ce ya yanke shawarar komawa bangaren tare da dubban magoya bayansa ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci na jam’iyyar da Abdullahi Abbas ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Babu ruwana da rikicinku na APC a Kano, Shugaba Buhari ya yi fashin baki

Hadimin Ganduje da dubban magoya bayansa sun koma sansanin Shekarau
Hadimin Ganduje da dubban magoya bayansa sun koma sansanin Shekarau Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Mista Shehu ya ce magoya bayansa sun yanke shawarar yin kamfen domin nasarar Sanata Barau Jibrin a kudirinsa na takarar gwamna, Daily Nigerian da Premium Times suka ruwaito.

Ya ce:

"Duk da cewar mafi akasarin mutane a karamar hukumar Nasarawa na tare da mu, bangaren da Abdullahi Abbas ke jagoranta sun yi kunnen uwar shegu da hakan, sannan suka goyi bayan sauran da basu da goyon bayan talakawa.
"Bari na fada maku cewa ba mu kadai bane a wannan tafiyar. Hadimai da manyan yan siyasa da dama sun fi karkata ga sahihin shugabancin jam’iyyar na Danzago, kuma mun yi na'am da takarar Sanata Barau Jibrin.
“Sanata Barau Jibrin mutum ne mai gaskiya kuma amintacce wanda kowa ya yarda da shi. Ba a tursasa shi kan mutanen Kano ba, sai dai su kansu mutanen ne suke son tursasa shi."

Kara karanta wannan

Korona ta barke a Aso Rock: Garba Shehu, Lai Mohammed, Dogarin Buhari duk sun kamu

Jaridar ta kuma rahoto cewa tun bayan da kotu ta sanar da bangaren Haruna Danzago a matsayin sahihin shugabancin APC, hadimai da magoya bayan gwamnan da dama sun fara komawa sansanin Shekarau.

Daga cikin wadanda suka yasar da Ganduje akwai tsohon mataimakinsa, Hafiz Abubakar da wani makusancinsa, Murtala Zainawa.

Babu ruwana da rikicinku na APC a Kano, Shugaba Buhari ya yi fashin baki

A gefe guda, mun ji cewa fadar Shugaban kasa ta yi fashin baki game da ikirarin da wasu yan siyasa a jihar Kano ke yi na cewa Shugaba Muhammadu Buhari na marawa wani tsagin baya.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya barranta maigidansa daga maganar marawa wani tsagi baya.

Ya bayyana hakan a jawabin kar ta kwana da ya saki da daren Asabar, 25 ga Disamba, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel