Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a Kwara, Ɗan a mutun Bukola Saraki ya sauya sheka zuwa APC

Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a Kwara, Ɗan a mutun Bukola Saraki ya sauya sheka zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP ta ɗauki matakin dakatarwa kan tsohon kwamishinan ilimi kuma ɗan amutun Saraki, Injiniya Musa Yeketi
  • Sai dai bayan faruwar haka, Misata Yeketi, ya bayyana ficewarsa daga PDP, tare da komawa jam'iyyar APC mai mulki a jihar
  • Fitaccen ɗan siyasan kuma tsohon na kusa da Bukola Saraki, ya tabbatar da matakin da ya ɗauka ne a wurin ɗaura auren ɗiyarsa

Kwara - Jam'iyyar PDP reshen jihar Kwara ta dakatar da tsohon kwamishinan ilimi, injiniya Musa Yeketi, bisa zargin cin dunduniyar jam'iyya ta bayan fage.

Daily Trust ta rahoto cewa Yeketi, tsohon ɗan gani kasheni ne na tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.

APC da PDP
Jam'iyyar PDP ta yi babban rashi a Kwara, Ɗan a mutun Bukola Saraki ya sauya sheka zuwa APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta dakatar da tsohon kwamishinan ne a wata wasika da gundumarsa a ƙaramar hukumar Asa, jihar Kwara ta fitar.

A wasiƙar mai ɗauke da sa hannun shugaban PDP na gundumarsa da kuma Sakatare, sun zargi jigon da aikata wasu ayyuka a gefe guda na yaƙi da jam'iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dakatarwan, kamar yadda wasikar ta bayyana, ya dace da sashi na 57 (3) na kundin dokokin jam'iyyar APC wanda aka yi wa garambawul.

Wane mataki ɗan siyasan a jihar Kwara ya ɗauka kan haka?

Amma biyo bayan wannan mataki na dakatar da shi, Mista Yeketi, a ranar Lahadi, ya fice daga jam'iyyar PDP a hukumance, ya koma All Progressive Congress (APC).

Tsohon kwamishinan na ilimi kuma fitaccen ɗan siyasa a Kwara ya yi amfani da wurin shagalin ɗaura auren ɗiyasa wajen sanar da matakin da ya ɗauka na sauya sheka zuwa APC mai mulki.

A wani labarin kuma Iyaye sun dawo daga kasar waje hutun shakatawa, sun taras ɗansu ya tafi yaƙi Ukraine

Wasu iyaye sun sha mamaki yayin da suka dawo gida daga hutun shaƙawa da suka tafi suka taras ɗan su baya nan .

Mahaifin matashin mai suna Adam, ya ce sun yi tsammanin zai zo ya ɗauke su a filin jirgi, amma sai faɗa musu ya yi ya tafi taimakawa Ukraine.

Asali: Legit.ng

Online view pixel