Da Dumi-Dumi: Yan Majalisar dokokin tarayya sun kaɗa kuri'a kan takarar Tinubu a 2023

Da Dumi-Dumi: Yan Majalisar dokokin tarayya sun kaɗa kuri'a kan takarar Tinubu a 2023

  • Mambobin majalisar dokokin tarayya na jam'iyyar APC sun tabbatar da goyon bayansu ga Bola Tinubu ya gaji Buhari
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar, Honorabul Ado Doguwa, ya ce lokaci ya yi da za'a saka wa Tinubu alherin da ya yi wa ƙasa
  • Ya nemi duk mai goyon bayan takarar Bola Tinubu, yace Aiyes, nan take kowa ya bayyana haka da karfi

Abuja - Mambobin jam'iyyar APC na majalisar dokokin tarayya sun goyi bayan takarar jagora, Bola Ahmed Tinubu, a babban zaben 2023 dake tafe, kamar yadda The Nation ta rahoto

A wani sakon murya mai ƙara, Mambobin majalisar sun faɗi 'Aiyes' ga kudurin tsohon gwamnan Legas lokacin da shugaban masu rinjaye, Alhassan Ado Doguwa, ya nemi a kaɗa kuri'ar jin ra'ayi.

Doguwa ya ce Tinubu ya taimakawa yan Najeriya da dama suka zama shugaban ƙasa, gwamnoni, Sanatoci, da mambobin majalisar wakilai, saboda haka, "Lokaci ya yi da zamu saka masa."

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Abin da Buhari yace da na fada masa inason na gaje shi, Tinubu ya magantu

Tinubu a Majalisa
Da Dumi-Dumi: Yan Majalisar dokokin tarayya sun kaɗa kuri'a kan takarar Tinubu a 2023 Hoto: Oluomo Akanbi Ade Afonja/facebook
Asali: Facebook

Doguwa ya ƙara da cewa yan majalisar wakilai na APC na goyon bayan jam'iyya ta damƙa wa Tinubu tikiti ya kare martabarta a zaben 2023.

A cewar shugaban masu rinjaye na majalisar, da yawan mambobin majalisa sun samu nasarar shiga Ofis ne saboda goyon bayan Tinubu.

Ya ce:

"Ina son kallon idon ka na faɗa maka lokaci ya yi da zamu saka maka. Tinubu ya taimaka wa mutane sun zama shugaban ƙasa, gwamna, Sanata da ɗan majalisar dokoki, babu wani lokaci da ya dace mu saka masa da ya wuce yanzu."
"Zamu cigaba da kasancewa a tare da kai domin cigaban Najeriya da al'ummar mu. Muna godiya mara adadi, zamu goyi bayanka har ka cimma burinka na rayuwa."
"Wani lokacin idan muna tattaunawa da mutane zaka ji suna faɗin shugaban ƙasa tsohon soja ne, amma kai daga nan zauren ka fita, kuma mun ƙagu Buhari ya miƙa wa shugaba na gaba wanda ya kware a harkar dokoki."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta fasa taron majalisar zartaswar gobe

Ba sai ka nemi goyon bayan mu ba dama a bayanka muke - Doguwa

Bugu da ƙari, Doguwa ya ce Tinubu ya zo neman goyon bayan waɗan da dama can suna tare da shi saboda gudummuwarsa ga cigaban Najeriya.

"Tamkar ace ka zo nan wa'azi ne ga waɗan da sun rika sun karɓi da'awarka saboda gudummuwar da ka bayar wajen cigaban ƙasa. Kai kaɗai muka sani kuma sai inda ƙarfin mu ya ƙare."

Domin tabbatarwa Tinubu goyon bayan yan majalisar dokoki, Ado Diguwa ya nemi a kaɗa kuri'ar jin ta bakin kowane mamba.

Mambobin majalisar na jam'iyyar APC suka faɗi Aiyes da karfi bayan ya nemi masu goyon baya sun faɗi haka.

A wani labarin na daban kuma Ɗiyar Bola Tinubu ta yi tsokaci kan shirin mahaifinta na gaje kujerar Buhari

Ɗiyar Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa mahaifinta ya shirya tsaf domin jan ragamar mulkin Najeriya a 2023.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ku bari Buni ya gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC, Buhari ya aike da wasika

Tinubu-Ojo, ta ce kowane abu kan samu matsala kuma ya warware, kamar haka ne mahaifinta ya yi rashin lafiya kuma ya warke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel