"Buhun Shinkafa da Atamfa Kawai aka Raba Mana Bayan Zabe," Shugabannin Matan APC

"Buhun Shinkafa da Atamfa Kawai aka Raba Mana Bayan Zabe," Shugabannin Matan APC

  • Shugabannin jam'iyyar APC mata a jihohin kasar nan 36 sun nuna bakin cikin yadda gwamnatin Bola Tinubu ta yi watsi da su
  • Shugabar matan, Misis Patricia Yakubu da ta jagoranci gangamin nuna goyon baya ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje ce ta bayyana hakan
  • Ta ce tun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kama aiki, turmin atamfa daya da buhun shinkafa ne kawai ya ratsa tsakaninsu da jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- A ranar Talatar nan ne shugabannin mata a jam'iyyar APC su ka fusata tare da dira sakatariyar jam'iyyar a babban birnin tarayya Abuja kan yadda su ka ce an ci moriyar ganga.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya yi watsi da mu bayan zaben 2023', shugabannin mata na APC sun koka

Matan da ke jagoranci a jihohin kasar nan 36 sun zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC da watsi da lamauransu bayan sun bayar da gudunmawa an ci zabe.

Mata a jam'iyyar APC
Mata a APC sun ce an yi watsi da su Hoto: Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

An manta da mata a jam'iyyar APC?

Daily Trust ta wallafa cewa matan na ganin tsantsar rashin adalci ne yadda ake ware su a APC duk da rawar da su ka taka a zaben da ya gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabar tafiyar, Mrs Patricia Yakubu, ta ce tun bayan nasarar a APC ta samu ba a sake waiwayarsu ba.

Ta ce atamfa da buhun shinkafa ce kawai ta shiga tsakaninsu da gwamnatin Tinubu.

Matan APC na goyon bayan Abdullahi Ganduje

Shugabar matan da ke rike shugabancin mata a jam'iyyar APC, Mrs Patricia Yakubu, ta jagoranci 'yan uwanta wajen nuna goyon baya ga Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban APC na kasa.

Kara karanta wannan

"Daurarru 400 a Kano ba su san makomarsu a gidan yari ba," Inji 'Yan Sanda

Ta ce amma suna da koke mai karfi, domin ya kamata ya sa baki kan yadda aka yi watsi da su a jam'iyyar, amar yadda Punch News ta wallafa.

Shugabar ta ce mata a jam'iyyar sun yi rawar gani wajen samun nasarar Bola Ahmed Tinubu, amma sun zama 'ya'yan bora.

Misis Patricia Yakubu, ta ce an sace dan guda daga cikinsu, sannan an rushe gidan wata duk a fafutukar da su ke na tabbatar da Tinubu ya kai ga ci.

Ta nemi Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanya baki wajen warware wannan matsala.

Shugaban APC ya fadi matsalar zabe

Mun kawo muku labarin yadda shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana wadanda ke kawo tarnaki a lokutan zabe a Najeriya.

Ya ce su da kansu 'yan siyasa ne ke dawo hayaniya da kawo matsalolin yayin zabukan kasar nan wanda hakan babbar matsala ce ga hukumar zabe ta INEC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.