Ki Rufa min Asiri: Fasto Yana Rokon Budurwa Kada ta Fitar da Bidiyon 'Sharholiyarsa'

Ki Rufa min Asiri: Fasto Yana Rokon Budurwa Kada ta Fitar da Bidiyon 'Sharholiyarsa'

  • 'Yan Najeriya sun yi tururuwa wajen yin tsokaci game da wata hirar sirri a Whatsapp na wata budurwa da wani fasto 'dan Najeriya da take masa barazana
  • Matar mai suna Okachi Jessica tayi faston barazana gami da yunkurin fallasa bidiyon sharholiyarsa idan bai bada N300,000 zuwa N500,000 ba
  • Jessica ta ce zata saki bidiyon nanayen ga dukkan mutanen da take dasu a Whatsapp gami da tura wa wani shakikin abokinsa wanda shima fasto ne

Dubun wata 'yar Najeriya mai suna Okachi Jessica ya cika bayan tayi wa wani fasto barazanar sakin bidiyon sharholiyar da yayi.

Charles Awuzie ne ya sanar da hakan a dandalin Facebook bayan ya wallafa hira tsakanin mai barazanar da wanda take yi wa barazana.

Fasto da budurwa
Ki Rufa min Asiri: Fasto Yana Rokon Budurwa Kada ta Fitar da Bidiyon 'Sharholiyarsa'. Hoto daga AaronAmat, Facebook/Charles Awuzie
Asali: Facebook

Jessica ta tura wa faston da ba a ambaci sunansa ba sako ta kafar sada zumuntar Whatsapp gami da masa barazanar tura wa wani fasto wanda abokinsa ne na kusa idan bai turo mata N300,000 zuwa N500,000 ba.

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Garzayo Najeriya Daga Turai Domin Haduwa Da Sahibinta, Bidiyonsu Ya Yadu

Faston yayi kokarin rokonta amma tayi kunnen uwar shegu. Yayin da ya gaza bata abun da ta bukata, ta kara yi masa barazanar turawa dukkan mutanen da take dasu a kafar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar Charles, faston ya nemi agaji. Charles ya kara da fallasa lambar wayar mai barazanar da bayananta na Facebook har da hotunanta, inda ya bukaci masu amfani da soshiyal midiya da su sanar mata da cewa ta cancanci a aika ta gidan yari.

"Dole ne mu dinga fallasa masu mana barazana."

- Kamar yadda ya rubuta.

Tsokacin jama'a

Abbas John Favour ta ce:

"Ina alawadai da barazana amma shima faston ya kamata ya san cewa zina na daya daga cikin abubuwan da majami'a ke kyamata. Idan yana so ya tuba da gaske, yaje ya nemi afuwa gami da gafarar Ubangiji idan har da gaske yayi imani."

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

Ndidiamaka Precious ta ce:

"Muma ya kamata mu yi kokarin ganin mun dena bawa mutane samun damar yi mana barazana. Wadannan masu barazanar basa da asara saboda dalilin wani abun kunya da mutum yayi. Tsaftacacciyar rayuwa ita ce nagarta."

Francis Udoka Ndimkoha ta ce:

"Yayin da muke caccakar mai barazanar, ya kamata mu shawarci fastoci da su zama na kwarai gami da rayuwa mai tsafta. Abun ba wai kawai yin lalata da bada kudi bane a'a har da kafa misali ga saura."

John Doreen Ogonna ta ce

"To fa. Ina ga lokaci yayi da wadannan shugabannin zasu yi kokarin danne maitar su don gudun irin wannan tozarcin.
"Ita kuma matar, ya kamata ta dandana kudarta. Ya kamata a dauki barazana a babban laifi a cikin al'umma tare da tanadar babban horo ga duk wanda aka kama."

Asali: Legit.ng

Online view pixel