Bobrisky: EFCC za ta Zurfafa Binciken Wasu Fitattun Mutane Kan Cin Zarafin Naira

Bobrisky: EFCC za ta Zurfafa Binciken Wasu Fitattun Mutane Kan Cin Zarafin Naira

  • Hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce yanzu haka tana binciken wasu jarumai bisa laifin cin zarafin naira
  • EFCC za ta gurfanar da wadanda ta kama dumu-dumu da laifin wulakantar da takardun kudin kasar nan gaban kotu domin a hukunta su
  • Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta samu nasarar gurfanar da fitaccen dan daudun nan Bobrisky a gaban kuliya, har aka yi masa daurin watanni shida ba tare da zabin tara ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Najeriya- Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta ce za ta ci gaba da zurfafa bincike kan wasu jarumai bisa laifin cin mutuncin naira da niyyar gurfanar da su gaban kotu.

Kara karanta wannan

Iftila'i: Mummunar gobara ta shafe kasuwar Boda dake Gaya

Dele Oyewale, jami'in hulda da jama'a na hukumar EFCC ne ya bayyana hakan, inda ya ce ba za su zuba idanu ana cin mutuncin naira ba.

Hukumar za ta kama wadanda ke wulakanta takaddar naira
Wasu daga jaruman da suka watsa kudi a taruka a baya Hoto: UGC
Asali: UGC

Wannan kuma na zuwa ne bayan EFCC ta samu nasara a kotu na daure shahararren dan daudun na, Bobrisky na watanni 6 ba tare da zabin tara ba saboda wulakanta takardar naira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Wadakar Deacon Famous

Deacon Famous, wanda asalin sunansa Udaya Awesome Chidiebere ɗan wasan barkwanci ne a Najeriya.

A shekarar 2023, ya ɗauki hankalin jama'a lokacin da aka gan shi yana watsa takardun kudin da aka ce ya kai Naira miliyan biyu a bikin ƙawarsa Ekene Umenwa.

2. Mawaki Wizkid da wulakanta naira

Mawaƙi da ya shahara a Najeriya ya janyo cece kuce a Disambar 2023.

An hango shi zaune a bayan mota yana watsa kuɗi kan titi, matafiya na ta rububin kwasar rabonsu.

Kara karanta wannan

An sake kai harin da ya yi sanadiyyar kashe mutane 10 a jihar Plateau, jama'a sun shiga firgici

3. Mawaki Davido ya watsa kudi

Shi ma Davido yana daga taurarin da ake sha gani yana watsa kudi a tarurruka, inda shi har dala ma yake watsawa.

A shekarar 2023, an hango Davido tare da Wizkid suna warwatsa kudi ga magoya bayansu a wani gidan shakatawa cikin nishadi.

4. Fati Washa

Fitacciyar jarumar Kannywood ɗin na daga jaruman da ke watsa kuɗi a tarurruka.

Wani bidiyo da aka ɗauka a 2021 ya nuna Washa na watsa kuɗi a a taron bikin ƙawarta.

5. Chief Priest

Chief priest shi ma shararren dan masana'antar nollywood, wanda ya ke tsohon shugaban kamfanin Cubana.

Shi ma ya shahara wajen watsa kudi a taruka da bukukuwa wanda ko a baya ya ja hankalin 'yan Najeriya matuka.

6. Oluwadarasimi Omoseyin

‘Yar Nollywood Oluwadarasimi Omoseyin, ita ma a shekarar 2023 an hango tana bushasha wajen warwatsa takardar naira wacce har ta kai hukumar EFCC ta cafke ta.

Kara karanta wannan

Bangaren maza ko mata? Hukumar Gidan Yari ta fadi sashen da za ta ajiye Bobrisky

A wancan lokaci, Leadership News ta ruwaito cewa har gidan gyaran hali aka tisa keyarta kafin a bayar da belinta akan naira miliyan biyar.

7. Eniola Badmus

Eniola Badmus, fitacciyar 'yar wasa ce a Nollywood, wacce ake yawan ganinta tana yawo ko harkokin biki da shahararren dan daudun nan Bobrisky.

An hango ita ma cikin wani bidiyo tana rausayawa da Bobrisky yayin suke watsa takardar naira a wani taron biki.

8.Portable Zazu

Habeeb Okikiola wanda aka fi sani da Portable ko Dr. Zeh na daga mawakan Najeriya dake daukar hankalin masoyansu, musamman yadda yake da son al’umma.

A kwanakin baya, an hango shi a jihar Ekiti yana watsa kudi a iska masoyansa kuma suna take masa baya a guje domin kwasar abinda za su iya samu.

Hukumar EFCC dai ta ce za ta fara kamawa da gurfanar da wadanda ake zargi da wulakanta takardar naira daga watan Fabrairun 7 2024, wanda shi ne lokacin da aka kafa ofishi na musamman kan yaki da cin mutuncin kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel