Karya Ta Kare: An Gano Gemu ya Cigaba da Fitowa Shahararren Dan Daudu Bobrisky

Karya Ta Kare: An Gano Gemu ya Cigaba da Fitowa Shahararren Dan Daudu Bobrisky

  • Bobrisky ya shiga komar hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati watau EFCC a can kwanakin baya
  • Amma yanzu wata 'yar soshiyal midiya ta gano fuskar bobrisky ta fara sauyawa yayin da yake ikirarin shi mace ne
  • A wasu hotuna da ta wallafa, ta ce gemu ya fara tsayawa Bobrisky bayan ya shafe kwanaki a ofishin EFCC bisa zargin wulakanta takardun kudin kasar nan
  • Bobrisky, wanda asalin sunansa Okuneye Idris Olanrewaju, ya kashe makudan kudi wajen sauya kamanninsa zuwa na mace

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Legas: Fitaccen dan daudun nan Okuneye Idris Olanrewaju, da aka fi sani da Bobrisky saboda yadda ya takarkare wajen sauya kammaninsa zuwa na mace ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan wata ta kyallaro shi ya fara gemu.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya rasu

A makon da ya gabata ne jami'an hukumar EFCC suka cafke Bobrisky da laifin cin mutuncin Naira, wanda aka kuma tabbatar da laifin kuma har yanzu yana hannun hukumar, kamar yadda legit ta ruwaito.

Tun bayan cafke Bobrisky, kanin tsohon Gwamnan jihar Ekiti da suke takun saka, Isaac Fayose ya ce a bayan kanta Bobrisky zai yi bikin sallah.

Bobrisky ya shahara bayan saura siffarsa zuwa ta mata
Bayan kashe makudan kudi wajen sauya siffarsa, an gano gemu ya fara tsayawa Bobrisky Hoto:Bobrisky
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bobrisky ya fara tsaida gemu?

Da alama tusa na neman kurewa bodari bayan da Bobrisky ya shafe kwanaki a hannun EFCC ba tare da ya yi gyaran fata ba kamar yadda yake bayyanawa a shafukan sada zumunta.

Wata mai amfani da kafar sadarwa ta wallafa a shafinta na instagram cewa tuni Bobrisky ya fara dawowa halittarsa ta namiji:

“Gemu ya fara tsayawa Bobrisky a hannun EFCC, ba za ka taba iya sauya halittarka ba."

Kara karanta wannan

Wuraren shakatawa 5 da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna

Kotu ta dauki mataki kan dan daudu

Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas dai ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare Bobrisky har sai an yanke hukunci kan tuhume-tuhumen da ake masa na wulakanta takardar kudin kasar nan.

Dan daudun ya amsa laifukan da ake zarginsa da su da suka hada da watsa takardun naira da cin mutuncinta, wanda hakan ya saba da dokar kasar nan.

Duk da amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, dan daudun ya ce bai ma san da dokar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel