Ku gina kan ku da zarar kun auri maza masu muƙami ko arziki, Toyin Lawani ta yi wa mata huɗuba

Ku gina kan ku da zarar kun auri maza masu muƙami ko arziki, Toyin Lawani ta yi wa mata huɗuba

  • Wata fitacciya a kafafen sada zumunta, Toyin Lawani ta shawarci mata akan kada su yi kasa a guiwa wurin gina kawunansu matsawar suka auri maza masu arziki ko mukami
  • A cewarta, in har mace ta zauna ba tare da tallafa wa kanta wurin zama wani abu ba, wata rana mijin zai yi amfani da damarsa wurin tozarta ta
  • Sannan ta kara da shawartar mata da su kasance masu wayau wurin zaben mijin aure, mace ta fahimci wanne irin mutum ne mijinta kafin ta aure shi

Wata sananniya a kafafen sada zumunta, Toyini Lawani ta shawarci mata akan kada su yi kasa a gwiwa wurin gina kawunansu idan sun auri maza masu mukami ko arziki, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tiwa Savage: Na so ace Dangote mahaifi na ne, amma kash

Ku gina kan ku da zarar kun auri maza masu muƙami ko arziki, Toyin Lawani
Toyin Lawani ta yi wa mata huduba: Ku gina kan ku da zarar kun auri maza masu muƙami ko arziki. Hoto: Toyin Lawani
Asali: Facebook

Kamar yadda tace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Idan kika auri miji mai arziki ko mulki kuma ba ki gina kanki ba, wata rana zai yi amfani da damarsa wurin wulakanta ki.”

Ya kamata mata su zama masu wayau

Ta kara da cewa:

“Mata ya kamata ku zama masu wayau kuma ku yi zaben miji tare da tunani. Ku san irin mutanen da za ku aura ciki da waje kafin ku fada tarkonsu.”

A cewar Toyin Lawani ta wata wallafa da ta yi a shafinta na Instagram, an hana Precious Chikwendu, tsohuwar sarauniyar kyau kuma tsohuwar mata ga tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ganin yaranta maza guda 4.

A wani bidiyo wanda Chikwendu ta saki a watan Disamban 2021, ta roki mata da su taimaka mata, inda ta ce kotu ta ba ta damar ganin yaranta amma ba a barinta yanzu haka ta gansu.

Kara karanta wannan

Tana wasa da lafiyarta: Bidiyon yadda wata mata mai ciki ta zaƙe wurin kwasar rawa da ƙarfinta na bara

Kamar yadda ta yi wa bidiyon lakabi: 'Sai an fara bin umarnin kotu kafin a fara sauraron muryar iyaye mata, kuma a daina amfani da yaranmu a matsayin harsashin cutar da bangare daya bayan rabuwar ma’aurata, za mu ci gaba da magana har sai an fahimci halin da yarana suke ciki.'

Babu uwar da ya dace ta fuskanci abinda Chikwendu ke fuskanta

Yayin tsokaci a kan bidiyon, Toyin Lawani ta ce:

“Babu uwar da ya dace ta fuskanci abinda @snowhiteey ta ke fuskanta a halin yanzu. Abin takaici, radadi da kuma mugunta.”

Ta kara da bayyana yadda aka dinga tura mata sakwanni kawai saboda ta sa baki akan abinda ya shafi tsohuwar sarauniyar kyau din.

A cewarta:

“Ana ta tsorata ni da wasu sakwanni. Har biya aka yi don a bata min suna matsayina na uwa saboda na yi magana da yawunta. Kowa ya san yadda nake a wurin yarana, don haka duk wanda zai yi soki-burutsunsa ya dade bai yi ba.

Kara karanta wannan

Bayan amsan N10m hannun saurayi, Bazawara tace ta fasa aurensa ana saura kwana 10 aure

“Idan na ga gaskiya sai na fadi. Ban taba sanin matar ba sai yanzu da nake ganin tana wallafa akan yaranta kullum, hakan yasa na tausaya mata saboda nima uwa ce. Ya kamata ko wacce uwa ta tsaya wa wannan matar har sai ta ci nasara.”

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Online view pixel