Wike Ya Fadi Abin da zai Sa Obi Ya Gudu a Najeriya ko Ya Ci Zaben 2027
- Ministan FCT, Nyesom Wike, ya soki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, inda ya bayyana cewa ba shi da ƙarfin gwiwar fuskantar matsalolin Najeriya
- Wike ya yi iƙirarin cewa maimakon Obi ya fuskanci ƙalubalen ƙasar, gudu zai yi zuwa ƙasar Kamaru idan har aka mika masa ragamar mulkin Najeriya
- Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake kiran mazauna sashen Abaji da ke Abuja da su sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya sake caccakar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, kan rashin ƙwarewa da dabarun gudanar da mulkin ƙasa.
Wike ya bayyana cewa Peter Obi ba shi da ƙarfin gwiwar fuskantar tarin ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, inda ya ƙara da cewa zai gudu ne kawai zuwa ƙasar Kamaru idan har aka ɗaura masa nauyin shugabancin ƙasar.

Source: Facebook
Punch ta rahoto cewa ministan ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Talata yayin taron haɗin gwiwa na ƙungiyar Rainbow Coalition da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar Abaji a birnin Abuja.
Kiran Wike ga masu zabe
Ministan ya jaddada cewa Najeriya tana buƙatar shugaba mai taurin zuciya da zai iya ɗaukar tsauraran matakai a lokuta masu wuya, kamar yadda shugaba Bola Tinubu ke yi, ba wai shugaban da zai gudu ya bar ƙasar a lokacin ƙalubale ba.
Ya bayyana cewa matsayin shugaban ƙasa ba wuri ne na wasan kwaikwayo na siyasa ko tallata kai kawai ba, a'a, wuri ne da ke buƙatar jajircewa, dabarun aiki, da kuma shirye-shiryen ɗaukar nauyi.
Vanguard ta rahoto Wike ya bayyana cewa:
“Bari in maimaita abin da na fada jiya. Ga mutanen Abaji, ta hanyar shugabansu, kansiloli da shugabanni, kun fito ne daga mazabu daban-daban. Kun gaya min za ku zaɓi Tinubu. Ba ni da matsala da hakan. Ina so in gani a akwati.”

Source: Facebook
Wike ya gargadi 'yan siyasa
Kazalika, ya gargaɗi shugabanni game da yi wa al'umma alƙawuran da ba za su iya cika su ba, inda ya ce zai auna su ne ta hanyar adadin ƙuri'un da suka samar wa shugaba Tinubu a mazabunsu a zaɓen 2027.
Wike ya ƙara da cewa birnin tarayya FCT dole ne ya doke jihar Rivers wajen samar da ƙuri'u a zaɓe mai zuwa, inda ya bayyana cewa zai gudanar da taro da matasan FCT a ranar Laraba don tsara dabarun haɗa kan jama'a.
APC ta caccaki Obi
A wani labarin, kun ji cewa jigon jam’iyyar APC na jihar Legas ya sha alwashin hana Peter Obi maimaita nasarar da ya samu a jihar a zaɓen 2023.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Legas, Cornelius Ojelabi, ya bayyana cewa sakamakon zaɓen da ya wuce ya zama katari ga jam’iyyar mai mulki wajen ƙarfafa dabarun yakin neman zaɓe.
Ojelabi ya kuma goyi bayan shirin ƙungiyar Rainbow Coalition da Ministan FCT, Nyesom Wike ke tallatawa, yana mai cewa ƙungiyoyin siyasa na da tasiri.
Asali: Legit.ng

