Tinubu Ya Yi Misali da Annabi Musa kan Batun Dawo da Tallafin Fetur

Tinubu Ya Yi Misali da Annabi Musa kan Batun Dawo da Tallafin Fetur

  • Mai girma Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba, domin a cewarsa Najeriya na fuskantar matsaloli
  • Shugaban ƙasar ya yi wannan bayani ne yayin ganawa da ƙungiyar City Boy Movement, inda ya nemi matasa su yaɗa manufofin gwamnatinsa
  • Tun bayan cire tallafin a watan Mayun 2023, farashin fetur ya tashi sosai, lamarin da ya ƙara tsadar rayuwa ga ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake bayyana matsayarsa kan dawo da tallafin man fetur.

Shugaba Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba, yana mai cewa matakin da ya ɗauka ya zama dole domin gyara tattalin arzikin ƙasar.

Tinubu ba zai dawo da tallafi ba
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 19 ga watan Oktoban 2026 yayin ganawa da ƙungiyar City Boy Movement, wadda matasa suka kafa domin yaɗa manufofi da tallafa wa gwamnatinsa, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamna Abba ya fito ya gayawa Tinubu abin da zai samu a Arewa a 2027

“Ina zuwa na cire tallafin man fetur tun a rana ta farko. Da ba haka ba, Najeriya za ta yi fatara, domin babu abin da ya rage na biyan tallafin,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yana jin maganganun ’yan adawarsa da ke alƙawarin dawo da tallafin man fetur.

Tinubu ya yi kwatanci da labarin Annabi Musa

Shugaban ƙasar ya yi amfani da misali daga koyarwar addini wajen bayyana dalilin da ya sa yake ganin ba za a koma tsarin tallafin man fetur ba, The Punch ta kawo labarin.

“Na tuna karatuna na Littafi Mai Tsarki da Alƙur’ani mai girma. Lokacin da Annabi Musa ya bar Masar, Tekun Bahar Maliya ya tsage ya ba shi hanya. Ba za ka ce wa Annabi Musa ya koma Masar ba. Da ƙarfinku da goyon bayanku, ba za mu koma Masar ba,” in ji Tinubu.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya yaba wa ƙungiyar City Boy Movement bisa ƙoƙarin da take yi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya ga gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: An ji yadda Buhari ya nuna akwai matsala idan Tinubu ya karbi mulki a 2023

Ya kuma buƙaci mambobinta su kai saƙonnin nasarorin da gwamnatinsa ta ce ta samu zuwa ga jama’a a matakin ƙasa.

Ya nemi matasa su yaɗa saƙon gwamnatinsa

Tinubu ya ce mutanen da ke aiki tare da shi sun ba shi kwarin gwiwar fuskantar zaɓe mai zuwa.

“Ku je jami’o’inku, kasuwanninku da ƙauyukanku. Ku tabbatar da cewa duk matashin da kuka sani yana da katin zaɓe na dindindin (PVC) kuma yana amfani da shi. Ku gaya musu abin da muka yi da abin da za mu yi. Ku yi yaƙin neman zaɓe da tunaninku,” in ji shugaban ƙasar.

Ya ƙarfafa matasa da su yi amfani da ra’ayoyinsu wajen yaɗa manufofin gwamnati da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin shiga harkokin zaɓe.

Cire tallafin man fetur da tsadar rayuwa

Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen tallafin man fetur ne a lokacin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a watan Mayun 2023.

Matakin ya jawo tashin farashin fetur cikin gaggawa, inda farashin lita ɗaya ya tashi daga ƙasa da Naira 200 zuwa farashin da ya kai kusan Naira 1,350 zuwa Naira 1,405 a manyan gidajen mai, kamar yadda bayanin da aka bayar ya nuna.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya zube kasa warwas a Najeriya saboda tsare tsaren Tinubu'

Manufofin cire tallafin sun fuskanci suka daga sassa daban-daban na al’umma saboda ƙarin tsadar rayuwa da suka biyo baya.

Sai dai shugaban ƙasar ya ci gaba da kare matakin, yayin da gwamnatin tarayya ke cewa cire tallafin ya zama dole domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa tana sa ran matsin tattalin arzikin da jama’a suka fara fuskanta zai ragu a hankali yayin da sauye-sauyen ke ci gaba.

Tinubu ya ce ba zai dawo da tallafi ba
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Su Kwankwaso za su dawo da tallafin fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi maganar dawo da tallafin man fetur.

Sanata Kwankwaso ya ce gwamnatin jam’iyyar ƙarƙashin Peter Obi za ta dawo da tallafin man fetur, amma ta wata hanya daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng