El Rufai Yana Ganin Ta Kan Shi a Kotu, Alkali Ya Amsa Bukatar ICPC a Shari’ar N10bn
- Kotu ta yi amince da bukatar lauyoyin ICPC na fito da bidiyo daga na’urar CCTV da aka ziyarci Nasir El-Rufai
- ICPC ta ce ganin faifan bidiyon zai taimaka wajen bayyana abin da ya faru a lokutan da ake takaddama a kai
- El-Rufai kuwa ya nemi a gabatar da cikakken faifan bidiyon da wasu bayanan ziyara domin a fahimci lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kotu ta amince da rokon da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta yi a shari’arta da Nasir El-Rufai.
ICPC tana shari’a da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya je kotu yana neman diyyar Naira biliyan 10.

Source: Facebook
ICPC ta mika bukata a shari'ar Nasir El-Rufai
The Nation ta ce Alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Chigozie Onah ya yi na’am da amfani da bidiyon na'urar CCTV.
Mai shari’a Chigozie Onah ya yanke hukuncin ne yayin da yake nazarin buƙatun da ɓangarorin biyu suka gabatar masa.
Sai dai kotun ta ƙi amincewa da buƙatar El-Rufai na nuna cikakken faifan bidiyon, wanda ya shafe sama da sa’o’i shida.
Maimakon haka, alƙalin ya ba kowanne ɓangare minti 20 domin nuna sassan bidiyon da suke ganin sun dace da shari’ar.
Alkali ya ki karbar bukatar lauyan El-Rufai
Alƙalin ya amince da hujjar lauyan ICPC, Yetunde Mosunmola, cewa nuna cikakken faifan a bainar jama’a barazana ne.
Ya ce hakan zai fallasa bayanan tsaro na hukumar tare da jefa cibiyarta cikin haɗari a Najeriya.
Yetunde Mosunmola Esq. ya nemi cewa idan akwai buƙatar kallon cikakken bidiyon, za a iya yin hakan a ɗakin alƙalin.
Kotun ta kuma ƙi amincewa da buƙatar El-Rufai na tilasta wa jami’an ICPC da suka gabatar da shaida da su bayyana a kotu.
Tsohon gwamnan yana so su bayyana ne domin a yi musu tambayoyi. A nan ma Chigozie Onah bai yi yadda mai kara yake so ba.
Kamar yadda The Guardian ta rahoto, El-Rufai ya shigar da ƙarar ne yana zargin ICPC da hana shi ganawa da matarsa.
Sai a Nuwamban 2026 za a koma kotu
Baya ga mai dakinsa, Aichatou Asabe, ya yi korafin an hana shi ganin ɗansa, Abba El-Rufai, a lokacin da yake tsare a IPCP.
Saboda haka tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya nemi kotu ta ba shi diyyar Naira biliyan 10.
Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 3 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron muhimman buƙatu a kotu.

Source: Facebook
Meyasa mutanen El-Rufai suka bar shi?
A nan aka ji labari Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu ya fadi musababbin rabuwar Nasir El-Rufai da wasu na hannun daman shi.
'Dan siyasar ya ce su suka kawo tsohon gwamnan siyasa tun farko, kuma suka dafa masa ya samu mulki a APC a shekarar 2015.
Bashir Sa’idu ya zargi Malam El-Rufai da cin amanar su a jam'iyyar ADC don haka suka koma wajen Gwamna Uba Sani da suka bari.
Asali: Legit.ng

