Pandora Papers: Yadda ‘Ya ‘yan Sambo Dasuki suka boye miliyoyin kudi a lokacin da yake ofis

Pandora Papers: Yadda ‘Ya ‘yan Sambo Dasuki suka boye miliyoyin kudi a lokacin da yake ofis

  • ‘Ya ‘yan Sambo Dasuki sun yi wa Hydropower Investments LTD rajista a boye
  • Attajirin ‘dan kasuwar nan, Leno Adesanya ya taimaka wajen kafa kamfanin
  • An kafa kamfanin a asirce a kasar ketaren ne domin a kauracewa biyan haraji

Sokoto - Wasu yara uku daga cikin ‘ya ‘yan Sambo Dasuki, daga ciki har da wasu matasa sun tara kadarori a boye da yake rike da mukami a gwamnatin PDP.

Daily Trust ta fitar da wani rahoto daga binciken Pandora Papers wanda wata kungiya ta ‘yan jarida masu binciken kwa-kwaf suka gudanar kwanan nan.

Binciken da kungiyar International Consortium of Investigative Journalists (ICIJ) tayi ya nuna cewa ‘ya ‘yan na Kanal Dasuki (rtd) sun guje wa biyan haraji.

Kara karanta wannan

Gwamnoni, jiga-jigan APC, PDP 7 da EFCC ke bincika kan batun Pandora Papers

Leno Adesanya ya taka rawar gani

An gano cewa a 2013 ne wani attajirin ‘dan kasuwan Najeriya, Leno Adesanya ya tuntubi wasu kamfanoni domin su yi wa iyalin Dasuki rajistar wani kamfani.

Takardun da aka samu sun nuna cewa Leno Adesanya ya taimaka wa ‘ya ‘yan tsohon hadimin shugaban Najeriyan wajen kafa Hydropower Investments LTD.

An kafa kamfanin da yarjejeniyar iyalin Dasuki za su sa hannun jari miliyan 1.5 a kamfanin Sino Africa (Nigeria) Limited, wanda su Adesanya ne suka mallaka.

Sambo Dasuki
Kanal Sambo Dasuki mai ritaya a kotu Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Hydropower Investments ya samu rajista

Jaridar tace takardun Hydropower Investments sun nuna kamfanin na da alaka da Sunrise Power & Transmission (Nigeria) da ke rikici da gwamnatin tarayya.

A watan Nuwamban 2013 aka yi wa Hydropower Investments rajista. Adesanya da Abubakar Atiku Dasuki (‘dan Dasuki) sune Darektocin wannan kamfanin.

Kara karanta wannan

Pandora Papers: An sake bankaɗo manyan kamfanonin gwamnan APC na 3 na ƙasar waje

Binciken dai ya tabbatar da cewa duk da Adesanya ne ya tsaya wa kamfanin, babu ko sisin shi a ciki. Wani gidan shi ne ma aka yi amfani a matsayin adireshi.

Abubakar Atiku Dasuki ne yake da hannun jari 17,000 a kamfanin. Hassan Sultan Dasuki ya zuba hannun jari 16,500, sai Asmau Iman Dasuki ta mallaki 16,500.

Sambo Dasuki yace ba shi ya aiki Adesanya ya yi wannan aiki ba. Sannan ‘ya ‘yan na sa Abubakar (31) da Asmau (18) da Hassan (18), sun mallaki hankalinsu.

Sunrise Power & Transmission Ltd

Idan za a tuna, kamfanin Sunrise Power & Transmission (Nigeria) Co. Limited ne ya kai gwamnatin Najeriya kotu a kan aikin wutan lantarkin Mambilla.

Kamfanin ya bukaci a biya shi kudi saboda saba yarjejeniyar da aka yi da shi a baya. Femi Falana ya tsayawa SPTCL, ya na neman Gwamnati ta biya diyyar $400m.

Kara karanta wannan

Sanusi, Minista za su jagoranci tattaro Biliyan 10 domin a bunkasa kiwon lafiya a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng