Aikin Hanyar Kano zuwa Abuja zai samar da Ayyuka sama da 3000 - Minista

Aikin Hanyar Kano zuwa Abuja zai samar da Ayyuka sama da 3000 - Minista

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunda Raji Fashola, ta kaddamar da aikin gyaran hanyar Kano zuwa Abuja.

Wani sabon rahoto da sanadin shafin jaridar The Nation ya bayyana cewa, wannan aiki da gwamnatin tarayya ta kaddamar zai samar da ayyuka sama da 3000 cikin shekaru uku masu gabatowa.

Karamin Minista na biyu na ma'aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Surv Hassan Zarma, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai inda ya bayyana cewa, baya ga samar da ayyuka na kai tsaye wannan aiki zai kuma samar da wadanda ba na kai tsaye ba akan babbar hanyar.

Aikin Hanyar Kano zuwa Abuja zai samar da Ayyuka sama da 3000 - Minista
Aikin Hanyar Kano zuwa Abuja zai samar da Ayyuka sama da 3000 - Minista

Ministan wanda ya gana da jaridar The Nation ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf domin ci gaba da malalo dukiya har zuwa kammala wannan babban aiki.

DUBA WANNAN: Buhari ya tursasa Obasanjo dawo da Kudaden Wutar Lantarki - Oshiomhole

A cewar sa, tuni kamfani mai rike da kwangilar wannan aiki, Julius Berger Plc, ya fara aikin gadan-gadan a sassa uku na hanyar babu kakkautawa, inda ya kara da cewa gwamnati ta kudiri inganta duk wani nakasun gine-gine a kasar nan.

Kamar yadda shafin jaridar Legit.ng ya ruwaito a ranar Talatar da gabata, ana sa ran kammala kwangilar aikin hanyar mai tsayin Kilomita 375.4 ta kimanin N155,470,626,078.07 cikin watanni 36 masu gabatowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng