Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

Yau Buhari Zai Bude Titin Kaduna-Kano, Gadar N/Delta da Wasu Manyan Ayyuka 8

  • Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu gadoji uku da gwamnatin tarayya ta gina a mulkinsa
  • Shugaban na Najeriya zai bude sashen hanyar Kaduna-Kano da ke kan babban titin Abuja-Kano
  • Gwamnatin tarayya ta kammala gina Hedikwatar hukumar Kwastam bayan shekara da shekaru

Abuja - A ranar Talatar nan, Mai girma Muhammadu Buhari zai kaddamar da gadar Neja da wasu muhimman ayyuka da gwamnatinsa ta kammala.

Wani jawabi da ya fito daga bakin Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya tabbatar da haka kamar yadda Tribune ta rahoto.

Mista Adesina ya ke cewa hakan ya nuna yadda gwamnatin mai gidansa ta maida hankali wajen samar da abubuwan more rayuwa a fadin kasar nan.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari da kayan sojoji Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Kwangilolin ma’aikatar ayyuka da gidajen da za a kaddamar sun hada da manyan gadoji, sakatariyar gwamnatin tarayya a jihohi uku da kuma titi.

Kara karanta wannan

Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sakatariyar gwamnatin tarayya

Sakatariyar farko ta na garin Awka a Anambra wanda ta ke dauke da ofisoshi, dakunan taro, banki, shagon abinci da abubuwa na zamani iri-iri.

Akwai wata sakatariyar Unguwar Dan Lawan a Zamfara, sai ta karshensu ta na jihar Bayelsa.

Jawabin Hadimin shugaban mai barin-gado ya ce tun 2005 aka fara shirin gina gadar, an yi hobbasa wajen yin aikin a 2014, amma abin bai yiwu ba.

The Nation ta ce sauran ayyukan sun hada da gadar Loko-Oweto da ta hada Jihohin Benuwai da Nasara da wata gadar Ikom Bridge a jihar Kuros Riba.

Titin da shugaban kasa Buhari zai bude a yau shi ne bangaren hanyar Kano zuwa Kaduna

Babban ofishin Kwastam

Baya ga haka, The Cable ta ce ana sa ran Mai girma shugaban kasa ya bude sabon Hedikwatar hukumar kwastam ta kasa da aka gina a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Bangarori 7 da Ake Jiran Bola Tinubu Ya Kawo Gyara Idan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Mataimakin shugaban kwastam, DCG Bashir Adeniyi ya ce wannan aiki da aka fara a 2002 ya ci N19.6bn, hedikwatar ta na nan ne a bayan ofishin NCC.

Nade-naden mukamai

A makon jiya, an samu labari Femi Adesina ya fitar da jawabi game da wasu nadin mukamai da shugaban kasa ya yi daf da zai bar karagar mulkin kasa.

Muhammadu Buhari ya sa-hannu domin tsawaita wa’adin masu sa ido a aikin FERMA sannan James Akintola ya canji Tunde Lemo da ya yi murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel